Wasu Ma’aikatan Gwamnati sun sace kudin yaki da barayi a Najeriya

Wasu Ma’aikatan Gwamnati sun sace kudin yaki da barayi a Najeriya

- Wasu manyan Darektoci sun sace makudan kudi a ma’aikatar ayyuka

- An shirya amfani da kudin ne ranar yaki da satar dukiyar Gwamnati

- Yanzu haka Alkali mai shari’a a Kotun ya dage karar zuwa watan gobe

Mun samu labari mai ban mamaki da takaici cewa an yi awon gaba da kudin da ake ware na fadakarwa game barayi da satar dukiyar Gwamnati a Najeriya. Wadanda su ka sace miliyoyin kudin sun shiga hannun Hukumar ICPC na kasar.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa Hukumar ICPC tayi ram da wasu manyan Darekta a Ma’aikatar ayyuka na Najeriya Mohammed Musa Abimiku da yayi facaka da wasu kudi da aka ware domin fadakar da Jama’a kan illar rashin gaskiya.

KU KARANTA: Ana neman wasu Turawa da aka sace a Jihar Kaduna

Rahoton ya bayyana cewa an yi gaba ne da sama da miliyan 4.5 cikin miliyan 5 da aka ware domin shirya ranar fadakwarwa ta Duniya a lokacin mulkin Shugaban Kasa Goodluck Jonathan. Cikin wanda aka kama akwai wani Darektan Micah Paman.

Yanzu haka dai maganar tana gaban Kotun Tarayya a Abuja inda ake neman Alkali ya yankewa wadannan manyan ma’aikata hukuncin da ya dace da su idan an kama su da laifi. Yanzu haka dai an bada belin su kan Naira miliyan 10 an kuma dage karar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng