Binance: Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Goyi Bayan Matakin da Shugaba Tinubu Ya Dauka

Binance: Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Goyi Bayan Matakin da Shugaba Tinubu Ya Dauka

  • An tsare wasu manyan jami'an kamfanin Binance guda biyu a Najeriya yayin da gwamnatin Bola Tinubu ke ƙoƙarin gyara tattalin arziƙin ƙasar nan
  • Biyo bayan tsare shugabannin kamfanin, Binance ya dakatar da cinikin Naira da kuɗin dijital na Bitcoin
  • Da yake mayar da martani kan wannan matakin, wani ɗan takarar shugaban ƙasa, Adamu Garba, ya bayyana cewa ya kamata a hukunta Binance

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Adamu Garba, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, a ranar Alhamis, 29 ga watan Fabrairu, ya ce ya kamata kamfanin Binance ya fuskanci hukunci.

Garba, jigo a jam’iyyar APC mai mulki, ya yi zargin cewa Binance ya aikata laifukan da suka saɓa wa dokar Najeriya.

Kara karanta wannan

Ana cikin halin kunci, Shugaba Tinubu ya aike da sako mai muhimmanci ga 'yan Najeriya

Adamu Garba ya goyi bayan Tinubu
Gwamnatin tarayya ta cafke jami'an kamfanin Binance Hoto: Bloomberg, Picture alliance
Asali: Getty Images

Ɗan jihar ta Adamawa ya haƙiƙance cewa Najeriya ba ƙasa ce mara doka ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Adamu ya ce kan cafke shugabannin Binance?

Ya bayyana hakan ne dai a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter).

"A cikin shekarar 2020 lokacin da ake tsaka da zanga-zangar EndSars, duk shirin da waɗannan kamfanonin kirifto ke yi shine su lalata tsarin kuɗin mu ta yadda mutane za su iya koma wajensu.
"Jack Dorsey ya zo da na shi dandalin yana fatan shi ma ya amfana da hakan.
"Najeriya ta zama ƙasa ta biyu mafi yawan masu amfani da kirifto a duniya, (ta farko ita ce Amurka) a waccan shekarar, inda aka yi hada-hadar Dala miliyan 526 a cikin wata guda.
"Kuma yanzu Binance, $26bn? Na P2P? Me suka ɗauke mu? Al'umma marar bin doka da oda? A’a! Lokaci ya yi da Najeriya za ta nuna cewa muna da dokoki kuma ƙasa ce mai shugabanci.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya keɓe minista 1, ya yaba masa kan yadda ya share hawayen ƴan Najeriya

"Binance ya kamata ya fuskanci hukunci kan saɓa wa dokokin Najeriya.”

Gwamnatin tarayya dai ta tsare aƙalla wasu manyan jami’ai biyu na kamfanin cinikayyar kirifto na Binance.

Illar Kirifto a Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa hadimin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Bayo Onanuga, ya yi magana kan illar da kirifto ke yi wa tattalin arziƙin Najeriya.

Bayo Onanuga ya yi nuni cewa da idan dai har ba a dakatar da harkar ba a Najeriya, za ta iya durƙusar da tattalin arziƙin ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng