Naira Miliyan 1 Muke So a Matsayin Mafi Karancin Albashi a Wata Inji Kungiyar NLC
- Shugaban kungiyar NLC a Ogun ya yi wa ma’aikata jawabi yayin da aka janye zanga-zangar lumanar gama-garin da aka shirya
- Hammed Ademola-Benco ya sake nanata cewa ma’aikata suna bukatar mafi karancin albashi ya zama akalla N1m a kowane wata
- Daga N38, 000 da aka tsaida, Kwamred Ademola-Benco yana so a ce babu ma’aikacin da bai tashi da Miliyan guda a karshen wata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abeokuta - Shugaban kungiyar ‘yan kwadago watau NLC na reshen jihar Ogun, Hammed Ademola-Benco, ya tabo batun albashi.
Kamar yadda Vanguard ta rahoto, Hammed Ademola-Benco ya ce ba su canza shawara a kan biyan akalla N1m a kowane wata ba.
Kungiyar NLC tana son albashin N1m a wata
A baya kungiyar kwadago tayi zancen cewa ya kamata duk wani ma’aikaci ya rika samun akalla miliyan a matsayin albashinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ‘yan kwadagon ya nuna suna nan a kan wannan matsaya, ba za su janye ba yayin da aka gama zanga-zangar lumuna.
Jawabin shugaban NLC a gaban ma'aikata
Kwamred Hammed Ademola-Benco ya yi wa abokan aikinsa ma’aikata jawabi dazu a garin Abeokuta, yana mai kira ga gwamnati.
‘Dan gwagwarmayar ya bukaci gwamnatin tarayya ta magance matsalolin rashin tsaro, yunwa da tsadar rayuwa da ake ciki.
Punch ta rahoto jagoran yana cewa ba za su janye bukatarsu na ganin an tsaida N1m ya zama karancin albashin ma’aikaci ba.
Ademola-Benco yana so daga N38, 000, gwamnati ta nunka mafi karancin albashin kasar duk da ba a biyan hakan a wasu jihohi.
Watakila wannan shi ne matsayar NLC ta reshen Ogun, bai nufin sauran kungiyoyin ma’aikata da ‘yan kasuwa su na tare da shi.
Akwai masu ra'ayin cewa ya kamata ma'aikaci ya samu akalla N200, 000.
NLC tana ikirarin ana bukatar wadannan makudan kudi ne la’akari da yadda farashin kaya suka tashi a mulkin Bola Ahmed Tinubu.
Bukatun NLC ga gwamnati
Mun kawo rahoton wasu bukatun da kungiyar NLC ta shimfidowa gwamnatin tarayya yayin da aka dakatar da zanga-zanga.
Idan ‘yan kwadago sun yi nasara, za a bude iyakoki domin shigo da abinci, kuma sun bukaci a kawo wasu matakan saukaka rayuwa.
Asali: Legit.ng