An Karrama Sojoji 8 da Suka Ƙi Karbar Cin Hancin Naira Miliyan 1.5 Daga Hannun Ɓarayin Shanu
- Rundunar soji ta karrama wasu dakarunta guda takwas da ke a OPSH na hudu saboda sun ƙi karbar ci hancin naira miliyan 1.5 a Plateau
- Rundunar a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba ta ce wasu ɓarayin shanu ne suka ba dakarun cin hanci bayan da aka kama su
- Kwamandan rundunar OPSH, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar wanda ya karrama dakarun ya yaba da rikon gaskiyar su
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Plateau - Dakarun atisayen Safe Haven (OPSH) da ke aiki a jihar Plateau da wasu sassan jihohin Arewa, sun ki amincewa da karbar cin hancin naira miliyan 1.5 daga wasu da ake zargin barayin shanu ne a Filato.
Jami’in yada labarai na rundunar Kyaftin James Oya ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Laraba a Jos.
Oya ya ce, sojojin da ke aiki a sashinsu na hudu, sun kama mutanen da ake zargin barayin shanu ne guda biyu wadanda suka ba su cin hancin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa jami'an takwas da suka ki karbar cin hancin ba kawai yabo kadai suka samu ba, har ma da tukuici daga kwamandan rundunar, Manjo-Janar Abdusalam Abubakar.
Abin da sanarwar ta kunsa
“Jami'an takwas da aka tura sashin OPSH na hudu, sun kama shanu 30 na sata a wani shingen bincike da ke kusa da Bisichi a karamar hukumar Barkin Ladi a jihar.
“Wadanda ake zargin, Anas Usman da Gyang Cholly nan take suka tunkari jami'an da nufin ba su cin hanci don su barsu su tafi da shanun da suka sato."
- A cewar sanarwar.
Oya ya ce kwamandan wanda ya yabawa sojojin bisa wannan jarumtaka, ya bukaci sauran jami’an tsaro da su yi koyi da hakan a wajen kare rayuka da dukiyoyi a jihar.
Karanta sanarwar a kasa:
Asali: Legit.ng