Dalilin da Ya Sa Na Kori Irukere a Matsayin Shugaban FCCPC, Tinubu Ya Fadawa Majalisar Dattawa
- Shugaba Tinubu ya ce Babatunde Irukera ba ya iya aiwatar da aikinsa yadda ya kamata, shi ya sa aka tsige shi daga shugaban hukumar FCCPC
- Shugaban kasar ya aike wa majalisar dattawa da wasikar dalilin tsige Irukera ne yayin da ya nemi amincewar majalisar wajen tabbatar da tsigewar
- Wannan mataki na tsige Irukera daga mukaminsa ya jawo cece kuce, inda baban lauya Femi Falana ya soki matakin shugaban kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa aka tsige Babatunde Irukere a matsayin shugaban hukumar kare masu amfani da kayayyaki ta tarayya (FCCPC).
Ya ce an cire Irukere ne saboda rashin iya gudanar da ayyukan ofishin sa yadda ya kamata.
Manufar yin garambawul a hukumomin gwamnati
Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da ya aikewa babban zauren majalisar domin neman amincewar tsige Babatunde Irukera daga shugabancin hukumar FCCPC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Tinubu ya ce ya zama wajibi a sake fasali tare da garambawul ga muhimman hukumomi na gwamnatin tarayya don ingancin aiki, AIT.Live ta ruwaito.
Ya kara da cewa matakin ya yi daidai da yunkurin gwamnatinsa na gudanar da nagartaccen mulki, da nufin kare hakkin masu amfani da kayayyaki a Najeriya.
An tsige Irukere bisa dokar hukumar FCCPC
Matakin zai kuma samar da ginshiki mai karfi na ingantacciyar gudummawar da manyan hukumomin gwamnatin za su ba da wajen bunkasa tattalin arziki a kasar.
Tsige Irukere da aka yi ya yi dai dai da tanadin sashe na 8(2) na hukumar gasar kasuwanci da kare masu amfani da kayayyaki ta tarayya (FCCPC), dokar 2018.
Tribune Online ta ruwaito mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya ce:
"An umurci Irukera da ya mika mulki ga babban jami’in hukumar, har sai an nada sabon shugaban hukumar."
Femi Falana ya soki Tinubu kan 'tsige' Irukera
Sai dai wasu manazarta sun zargi shugaban kasar da karya dokar kafa hukumar bayan da ya cire Irukera daga shugabanta.
Fitaccen lauya kuma mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Femi Falana, ya yi Allah wadai da tsige Irukera kamar yadda PM News ta ruwaito.
“Abin ban haushi ne amfani da kalmar ‘tsigewa’ wajen sallamar Irukera alhalin bai aikata wani laifi ba ko kuma zarginsa da ya aikata ba dai-dai ba."
- A cewar Falana.
Majalisar dattawa za ta binciki gwamnatin Yar'Adua, Jonathan da Buhari
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa majalisar dattawa ta kafa kwamiti da zai binciki yadda aka fitar da dala miliyan 496 don farfaɗo da kamfanin karafa na Ajaokuta.
Rahotanni sun bayyana cewa an fitar da kudin ne a tsakanin shekarar 2008 zuwa yau, kuma har yanzu kamfanin bai soma aiki ba duk da kashe makudan kudade a kansa.
Majalisar ta ba kwamitin wa'adin makonni biyu don gabatar mata da rahoto kan binciken badakalar kudaden.
Asali: Legit.ng