Sanatoci Sun Kafa Kwamiti Ya Binciki Bashin da Gwamnatin Buhari Ta Dumbuzo a CBN

Sanatoci Sun Kafa Kwamiti Ya Binciki Bashin da Gwamnatin Buhari Ta Dumbuzo a CBN

  • Majalisar dattawa ta samar da kwamiti na musamman da zai duba bashin da gwamnatin tarayya ta karbo a hannun CBN
  • Sanata Barau Jibirin ya sanar da haka da ya jagoranci zaman majalisa a jiya, ya ce za a kammala binciken a makonni hudu
  • Mataimakin shugaban majalisar dattawa ya ce bashin da gwamnatin Buhari ta ci ya jawo tashin farashin kaya a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A ranar Talata, majalisar dattawa ta kafa wani kwarya-kwaryan kwamiti da zai yi bincike kan bashin da CBN ya ba gwamnati.

Ana da labari cewa a lokacin Muhammadu Buhari yana ofis, ya karbi aron kusan N30tr a hannun babban bankin Najeriya na CBN.

Buhari
Sanatoci za su binciki bashin gwamnatin Buhari a majalisa Hoto: Nigerian Senate/Buhari Sallau
Asali: Facebook

Barau Jibrin ya kafa kwamitin bincike

Kara karanta wannan

Sabon gwamnan CBN da tawagarsa ne suka jefa ƴan Najeriya cikin tsadar rayuwa? Gaskiya ta fito

This Day ta ce mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ya jagoranci zaman majalisa, kuma ya kafa kwamitin bincike.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jiya Sanata Barau Jibirin ya sanar da wadanda ke cikin wannan kwamiti da zai yi bincike na musamman a kan bashin da aka karbo.

Sanatan jihar Kogi ta Yamma, Jibrin Isah ne zai jagoranci kwamitin binciken, Jibrin ya ce zai gama duk aikinsa cikin makonni hudu.

Illar bashin da Buhari ya karbo a CBN

Rahoton ya nuna a karshen watan Maris kwamitin zai gabatar da rahotonsa a zauren majalisa, daga nan sai a dauki matakin da ya dace.

Ana fama da tsadar rayuwa da hauhawar farashin kaya, mataimakin shugaban majalisar ya ce cin bashin yana cikin silar matsalar.

Ana so sanatocin suyi bincike da kyau musamman ganin yadda ake zargin yawan kudin da yake yawo ya jawo tsadar kaya a kasuwa.

Kara karanta wannan

Abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da rahoton Oronsaye

Idan kuma gwamnatin tarayya ba ta biya wannan kudi da ta karbi aro ba, Jibrin ya ce za a cigaba da lissafi da shi cikin bashin CBN.

Sanatocin da za su binciki bashin N30tr

'Yan kwamitin sun hada da Sanata Sani Musa; Sanata Solomon Adeola; Sanata Ekpeyong Asuquo da Sanata Mohammed Monguno.

Kamar yadda Premium Times ta rahoto akwai Sanata Victor Umeh, Sanata Aliyu Wadada, Sanata Abdul Ningi da Sanata Ipalibo Harry.

...mutane suna wahala a yau

Ana da rahoto tsarin cire tallafin fetur da aka yi a farkon mulki da daidaita kudin waje ya jawo ana kuka da gwamnatin Bola Tinubu.

Wahalar rayuwar da aka shiga ya jawo wasu sun fara maganar juyin mulki, manya da suka ga jiya da yunwa sun gargade su kan hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng