Hotunan Yadda Kanawa Suka Karade Titunan Kano a Zanga-Zangar Kin Jinin Tsadar Rayuwa

Hotunan Yadda Kanawa Suka Karade Titunan Kano a Zanga-Zangar Kin Jinin Tsadar Rayuwa

  • Mambobin kungiyar kwadago ta kasa sun bayar da hadin kai sosai yayin da ake ci gaba da zanga-zangar tsadar rayuwa a kasar
  • A jihar Kano, 'yan kwadago sun mamaye titunan babban birnin domin yin tattakin adawa da mawuyacin halin da 'yan Najeriya ke ciki
  • Zanga-zangar za ta ci gaba har zuwa ranar Laraba, 28 ga watan Fabrairu, yayin da talakawan kasar ke wahala wajen ciyar da kansu

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Kano - Kungiyar kwadago ta kasa ta gudanar da zanga-zanga a fadin Najeriya saboda tabarbarewar tattalin arziki a kasar.

Zanga-zangar da aka fara a ranar Talata, 27 ga watan Fabrairu za ta ci gaba har zuwa ranar Laraba, 28 ga watan Fabrairu.

'Yan kwadago sun fito da karfinsu a jihar Kano
Hotunan Yadda Kanawa Suka Karade Titunan Kano a Zanga-Zangar Kin Jinin Tsadar Rayuwa Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Mambobin kungiyar kwadagon sun bayar da hadin kai sosai yayin zanga-zangar da ta gudana a jihar Kano, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

"Akwai yunwa a kasar": Gwamnan PDP ya shiga zanga-zangar 'yan kwadago a jiharsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gano yadda 'yan kwadagon suka mamaye manyan tituna a birnion Kano domin nuna bacin ransu kan tsadar rayuwar da ake ciki a kasar.

Ga karin hotuna a kasa:

'yan kwadago sun yi zanga-zanga kan tsadar rayuwa
Hotunan Yadda Kanawa Suka Karade Titunan Kano a Zanga-Zangar Kin Jinin Tsadar Rayuwa Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

'Yan kwadago sun yi zanga-zanga a Kano
Hotunan Yadda Kanawa Suka Karade Titunan Kano a Zanga-Zangar Kin Jinin Tsadar Rayuwa Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Gwamna Makinde ya shiga zanga-zangar NLC

A gefe guda, mun ji cewa gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya shiga cikin 'yan kwadago da suka gudanar da zanga-zanga a garin Ibadan, a ranar Talata, 27 ga watan Fabrairu.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, a wajen zanga-zangar, Gwamna Makinde ya yarda cewa ana fama da yunwa a kasar.

A cewar gwamnan na Oyo, wahalar da ake sha a kasar ya kai kololuwa, inda mutane da dama basa iya ciyar da kansu.

'Yan Ibo sun ki shiga zanga-zangar tsadar rayuwa

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta rahoto cewa yayin da ake ci gaba da zanga-zanga a fadin Najeriya, wata kungiya a yankin Kudu maso gabashin Najeriya ta fadi dalilin kin shiga zanga-zangar.

Kara karanta wannan

Wata sabuwar zanga-zanga ta barke a sakatariyar jam’iyyar APC kan wani dalili 1 tak

Kungiyar mai suna South East Development Peace Initiative (SPDI) ta shawarci kabilar Igbo a Najeriya da su gujewa zanga-zangar.

Ta ce duk da halin kunci da suke ciki a yankin, ‘yan kabilar sun ki shiga zanga-zangar inda hakan ya jawo kace-nace, cewar Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng