An Kama Kasurgumin Mai Garkuwa da Mutane da Ya Addabi Babban Birnin Tarayya Abuja
- Rundunar ƴan sanda ta kama kasurgumin mai garkuwa da mutane wanda har Nyesom Wike ya saka ladar miliyoyin kudi idan aka kama shi
- Jami'an rundunar na FCT, Abuja ne suka kama mai garkuwar ake kira da Abu Ibrahim a dajin Sardauna da ke Toto, jihar Nasarawa
- Tawagar Abu Ibrahim ce ke da alhakin kai manyan hare-haren garkuwa da mutane ciki har da kashe Barista Agidy da mai sarauta Yahaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
FCT, Abuja - Jami’an rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja sun cafke mai garkuwa da mutane Samaila Wakili Fafa wanda aka fi sani da Abu Ibrahim
Habu Ibrahim shi ne na biyu cikin masu garkuwa da mutane biyu da ake nema ruwa a jallo, wadanda ministan FCT, Nyesom Wike ya ba da ladan N20m idan aka kama su.
Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, a cikin wata sanarwa a ranar Talata, ta ce an kama Abu Ibrahim ne a ranar 24 ga Fabrairu, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike ya saka ladar N20m idan aka kama Abu Ibrahim
The Nation ta ce an kama Ibrahim ne da misalin karfe 7:05 na yamma, bayan da jami’an tsaro da ke aiki da sahihan bayanan sirri suka kai farmaki dajin Sardauna da ke Toto, jihar Nasarawa.
A ranar Laraba, 14 ga Fabrairu, 2024, Wike, ya bayar da ladan naira miliyan 20 ga wanda ya gano mabuyar ‘yan bindigan guda biyu; Dahiru Adamu da Abu Ibrahim.
A baya dai rundunar ‘yan sandan da ke yaki da masu garkuwa da mutane a Abuja ta kama Saidu Abdulkadir aka Dahiru Adamu a ranar 15 ga Fabrairu, 2024.
Ayyukan ta'addancin da tawagar Abu Ibrahim ke yi
Adeh a cikin wata sanarwar, ta ce mai garkuwa da mutanen ya amsa cewa kungiyar sa ke shirya garkuwa da mutane da dama a babban birnin tarayya Abuja da kewaye.
Su ne suka sace Chris Agidy, hadimin Sanata Ned Nwoko da kuma Mista Sunday Yahaya Zakwai, hakimin kauyen Ketti, wadanda daga baya aka kashe su, in ji Tribune Online.
Ta kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan Abuja, CP Benneth Igwe, ya jaddada kudirin sa na yakar miyagun laifuka da kuma tabbatar da tsaron mazauna yankin.
Asali: Legit.ng