Waiwaye adon tafiya: Mata ne ke mulkin masarautar Daura kafin zuwan Bayajidda, Duba jerin sunayen su
Sabanin abinda muka saba gani a yanzu, inda maza ne zalla ke mulkin masarautu ko gadar sarauta, a baya tarihi ya nuna cewar mata sun yi mulki a kasar Hausa.
Kamar yadda tarihi ya tabbatar, kafin zuwa Bayajidda kasar Hausa (masarautar Daura), mata ne kawai ke yin mulki a masarautar Daura.
A cikin matan da suka yi mulki a masarautar ta Daura, anfi sanin sarauniya 'Daurama' wacce kuma a lokacin mulkinta ne Bayajidda ya zo masarautar har ta kai daga bisani sunyi aure.
Wasu masu nazarin tarihin masarautun Hausa na alakanta ficen da sunan sarauniya Daurama ta yi da cewar ita ce mace ta karshe da ta mulki masarautar Daura. Kuma tun bayanta har yanzu maza ne ke mulki.
Wata sarkakiya da har yanzu ba a iya warware ta ba ita ce yadda mata suka zama sune ke mulkin masarautar Daura.
DUBA WANNAN: Banyi nadamar rabon kaskon suya ga jama'a ta ba - Sanatan Najeriya
Abin tambayar shine; dama mata ne suka kafa masarautar tun farko ko kuwa sun gada ne daga wurin wani namiji kuma suka ki mayar da ita hannun maza?
Ga jerin sunayen sarauniyoyi takwas (8) da suka taba mulkar masarautar Daura a jere, ba tare da namiji ya karba ba:
1. Yakani
2. Tabwai
3. Yakanu
4. Waizam
5. Waiwa
6. Gidirgidir
7. Nagira
8. Daurama
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng