"Ba Maganar Albashi Bane" Ƴan Ƙwadago Sun Bayyana Abu 1 da Ya Sa Suka Fito Zanga-Zanga a Najeriya
- Ƴan kwadago sun bayyana cewa babban dalilin wannan zanga-zanga da mambobi suka fito shi ne yunwar da ƴan kasa ke ciki
- Joe Ajaero ya ce batun mafi ƙarancin albashi abin dubawa ne amma ba shi ne asalin abinda ya haddasa NLC fara zanga-zangar kwana biyu ba
- Shugaban NLC na ƙasa ya ce majalisar dinkin duniya ta ce akalla dala biyu zata ciyar da mutum ɗaya a kowace rana a yanzu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC) ta bayyana cewa mambobinta sun fara zanga-zangar kwanaki biyu ne sabida halin yunwar da ƴan Najeriya suka shiga.
Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, NLC ta ce wannan zanga-zangar da suka fara ba ta da alaƙa da batun sake duba mafi ƙarancin albashin ma'aikata.
Duk da gwamnatin tarayya ta zauna da ƙungiyar kwadago NLC domin daƙile wannan zanga-zanga, taron na su ya karkare ba tare da samun matsaya ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Menene maƙasudin zanga-zangar NLC?
Da yake jawabi ranar Talata, shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce sabanin yadda wasu ke ikirari, kungiyar ba ta tsiri wannan zanga-zangar kawai kan a ƙara mafi karancin albashi na N30,000.
Yayin da yake hira da manema labarai a Abuja, Ajaero ya ce:
"Ya kamata ku fahimci cewa muna wannan zanga-zanga ne saboda yunwar da ake fama da ita, wane hali waɗanda ba su samu aiki ba suke ciki? Yaushe za a ƙarƙare batun mafi ƙarancin albashi?"
"Wane sabon mafi karancin albashi za a kawo wanda zai magance yunwa? Majalisar ɗinkin duniya ta ce kowane mutum mafi talauci ya kamata a ciyar da shi akan dala 2 a kowace rana.
"Wannan shine mafi talauci. Kuma idan kana da iyali mai mutum shida, $2 a kowace rana sau shida, ya kama dala 12 kenan. A wata ɗaya ya kama $360, ma'ana N700,000 a kuɗin Najeriya."
Shugagan NLC ya kara da cewa wannan adadin kuɗin ne zasu rike mutum mai iyalai 6 a wata ɗaya wanda a yanzu mafi ƙarancin albashi shi ne N30 000.
A rahoton The Nation, Ajaero ya ci gaba da cewa:
"Kamar yadda kuka sani bamu zamu faɗa musu yadda zasu yi ba, iya ka dai mu gaya musu yadda muke ji ana fama da yunwa a ƙasar nan."
Ƴan kwadago sun kutsa NASS
A wani rahoton Masu zanga-zanga sun yi tururuwa a majalisar dokokin tarayya domin nuna bacin ransu kan halin da ake ciki na tsadar rayuwa a Najeriya.
Shugaban 'yan kwadago ta kasa, Joe Ajaero ne ya yi wa mambobin kungiyarsa jagoranci inda suke kokarin isar da kokensu ga shugabannin majalisar.
Asali: Legit.ng