An Yi Garkuwa da Shaidun Zaben Gwamnan Kogi a Harabar Kotun Abuja

An Yi Garkuwa da Shaidun Zaben Gwamnan Kogi a Harabar Kotun Abuja

  • A yayin da ake ci gaba da sauraron shari'ar zaben gwamnan jihar Kogi, ƴan bindiga sun sace shaidu biyar na jam'iyyar Action Alliance
  • An sace shaidun ne a harabar cibiyar shari'a ta ƙasa da ke Abuja, inda kotun sauraren kararrakin zaben jihar Kogi ke da zama
  • Dan takarar jam'iyyar A.A, Olayinka Braihmoh ya shaida cewa ƴan bindigar sun ci zarafin shaidun sun kuma lalata motoci yayin harin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Wasu da ake zargin ’yan bangar siyasa ne dauke da makamai sun yi awon gaba da mutane biyar da aka shirya za su ba da shaida a kan zaben gwamnan Kogi.

Jam’iyyar adawa ta Action Alliance ce ta ke kokarin gabatar da su matsayin shaida a gaban kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Kotu ta ba MTN, Airtel da Glo umarnin abin da za su yi da layukan da ba su da NIN

Braimoh ya yi zargin cewa an ci zarafin shaidun tare da lalata motar jigilarsu
Braimoh ya yi zargin cewa an ci zarafin shaidun tare da lalata motar jigilarsu zuwa kotu. Hoto: Olayinka Braimoh
Asali: Facebook

Braihmoh ya magantu kan harin

Dan takarar jam’iyyar Action Alliance, Olayinka Braihmoh ne ya shigar da karar kan zaben da aka yi a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023 a jihar, Kogi Reporters ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce an sace shaidun ne a harabar cibiyar shari’a ta kasa da ke Abuja, inda kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan Kogi ke da zama.

Braihmoh ya shaidawa ait.live cewa an ci zarafin wadanda aka sace kuma an yi wa ‘yan uwansu barazana, saboda jajircewarsu wajen ba da shaida kan zaben.

Yan sanda sun ceto shaidu hudu

Ya yi ikirarin cewa har yanzu ba a san inda shaidun suke ba, yayin da maharan suka lalata motocin da ke jigilar shaidun zuwa kotun.

Ya zuwa lokacin da aka rubuta wannan rahoto, an tattaro cewa ‘yan sanda sun ceto mutum hudu daga cikin wadanda abin ya shafa, yayin da daya ke hannun CID a Lokoja.

Kara karanta wannan

Kungiyar kwadago ta fara gudanar da zanga-zangar gama gari kan tsadar rayuwa

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, Josephine Adeh ta bayyana a wata tattaunawa ta wayar tarho cewa rundunar ba ta da masaniya kan harin.

INEC ta sanar da wanda ya lashe zaben gwamnan Kogi

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa hukumar zabe (INEC) ta ayyana Usman Ododo na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben jihar Kogi.

INEC ta ce Ododo ya lashe zaben ne bayan da ya samu kuri'u 446,337 wanda ya ba shi damar lallasa abokin gamayyar sa na SDP, Murtala Ajaka wanda ya samu kuri'u 259,052.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.