Yan Sanda da Sojoji Sun Yi Ƙazamin Artabu da Ƴan Bindiga, Sun Samu Nasara a Jihar Arewa
- Ƴan sanda da sojoji sun nuna wa ƴan bindiga banbanci, sun fatattake su tare da ceto mutum 10 da suka yi yunƙurin garkuwa da su a Katsina
- Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Abubakar Aliyu, ya ce jami'an tsaro sun samu wannan nasara ne ranar Lahadi da ta gabata
- Kwamishinan ƴan sandan jihar ya yaba da kokarin jami'an tsaro kana ya roƙi al'umma su ci gaba da ba su haɗin kai da bayanan sirri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Rundunar ƴan sanda ta jihar Katsina da haɗin guiwar dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar ceto mutum 10 da aka yi garkuwa da su a jihar.
Jami'an tsaron sun daƙile yunƙurin kai harin ƴan bindiga tare da ceto mutanen a ƙauyen Kukar Babangida da titin Yan Gayya Feeder a jihar Katsina.
Channels tv ta ce an samu wannan nasara ne ranar Lahadi, 25 ga watan Fabrairu, 2024 lokacin da haɗakar jami'an tsaron suka fita sintiri da misalin ƙarfe 10:00.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da jami'an tsaron ke zaylgayawa a titin Feedar, kwatsam ƴan bindiga ɗauke da miyagun makamai irinsu Ak-47 suka buɗe musu wuta.
Nan take gwarazan jami'an ƴan sanda da sojojin suka maida martanin luguden wuta mai ƙarfi, wanda ya sa suka yi nasarar daƙile harin tare da ceto mutum 10.
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Katsina, Abubakar Aliyu, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
CP ya yabawa jami'an tsaro
Sanarwar ta kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Aliyu Musa, ya yabawa yadda jami’an suka nuna gwarzantaka da jajircewa.
Ya kuma bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da bayar da goyon baya ga rundunar ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro a Katsina.
Ya kuma roki jama'a su rika kai rahoto da bayanai kan lokaci domin daukar matakin gaggawa kan duk wani nau’in aikata laifuka da hare-haren ƴan ta'adda a jihar.
Ya kuma kara jaddada kudirin rundunar ƴan sanda na tabbatar da kwanciyar hankali da tsaro a jihar Katsina, rahoton jaridar News Africa ya tabbatar.
Mutanen kauyuka 10 sun gudu daga gidajensu
A wani rahoton na daban Ƴan bindigan daji sun raba mutanen kauyuka aƙalla 10 daga gidajensu da gonakin su a ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.
Wani shugaban al'umma a ɗaya daga cikin ƙauyukan, Malam Jafaru Anguwar Salahu, ya ce yanzu sun koma ƴan gudun hijira a wasu yankunan.
Asali: Legit.ng