Matashi Ya Bugo Keke Daga Jihar Benue Don Ziyartan Ahmed Musa a Gidansa
- Ahmed Musa ya cika da farin ciki yayin da ya tarbi wani mutum da ya tuko keke daga jihar Benue don kawai ya gan shi
- A wata wallafa da ya yi a Instagram, Ahmed Musa ya dauki hoto tare da mai keken lokacin da ya isa gidansa
- Kyaftin din na Super Eagle ya ce ziyarar da mutumin ya kai masa yana da matukar muhimmanci a gare shi, musamman idan aka duba kokarin da ya yi
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Wani mutumi ya tuko keke tun daga jihar Benue har zuwa gidan Ahmed Musa don kawai ya hadu da shi su gaisa.
Kyaftin din ma Super Eagle ya wallafa hotunansa da matashi mai keken a dandalin Instagram.
Da yake yada hotunan, Ahmed Musa ya ce ziyarar da mutumin ya kai masa tana da matukar muhimmanci a gare shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya mika godiya ga masoyin nasa kan wannan dumbin soyayya da ya nuna masa ta hanyar tattaki daga wuri mai nisa don ganisa.
Ya rubuta:
"Babban jinjina ga wannan masoyi da ya tuka keke tun daga jihar Benue don kawo mani ziyara! Sadaukar da kai da goyon bayanka yana nufin duniya a gareni! Na gode da soyayyar da ka nuna mani!"
Masu amfani da soshiyal midiya sun taya mai keken murnar ganin Ahmed Musa.
Kalli wallafar a kasa:
Jama'a sun yi martani
@jay_bichi ya ce:
"Amma ka gargade shi kada ya sake irin haka don kada ya yi tunanin sabon hanyar samun kudi ne kuma mutane masu kirki irin ka ne ma za su iya kallonsa Allah ya kara albarka, kyaftin."
@nazeefe.wudil ya ce:
"Ka cancanci fiye da wannan soyayyar gwamna."
@a4dabledesigns ya ce:
"Ka cancanci duk wani abun alkhairi da ya zo hanyarka."
@comrshuaib ya yi martani:
"Mutane da dama za su fara wannan tafiyar kwanan nan."
Taurarin Super Eagles sun ziyarci Sarkin Kano
A wani labarin, mun ji cewa kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa da mai tsaron baya, Shehu Abdullahi, sun kai ziyara ta musamman fadar mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero.
Wannan ziyarar na zuwa ne yan kwanaki bayan kungiyar Super Eagle ta sha kaye a wasan karshe na gasar cin kofin Afrika (AFCON) a Ivory Coast a ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu.
Asali: Legit.ng