Akwai Matsala: Zanga-Zanga Mai Muni Ta Ɓarke a Jihohi Guda 2 Kan Muhimmin Abu 1
- Fararen hula sun bazama kan tituna zanga-zanga kan tsadar rayuwa a jihohin Edo da Osun ranar Litinin, 26 ga watan Fabrairu, 2024
- Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan zanga-zangar da aka yi a Ibadan, babban birnin jihar Oyo duk kan halin da mutane suka shiga
- A jihar Edo, an ga ɗan takarar gwamna karkashin inuwar NNPP a cikin masu zanga-zangar, sun aike da saƙo ga Tinubu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Kungiyoyin fararen hula a jihar Edo sun mamaye kan titunan suna zanga-zanga a Benin City, babban birnin jihar, ranar Litinin, 26 Fabrairu, 2024.
A rahoton Channels tv, mambobin ƙungiyoyin fararen hular sun kuma fantsama zanga-zanga makamanciyar wannan a Osogbo, babban birnin jihar Osun.
Masu zanga-zangar sun bazama kan tituna ne domin nuna takaicinsu kan matsin tattalin arzikin da yanzu haka ya jefa ƴan Najeriya cikin ƙuncin rayuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan zanga-zanga da ke gudana a Benin da Osogbo ta zo ne kwanaki kaɗan bayan wacce mazauna suka yi a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Ɗan takarar gwamna ya fita zanga-zanga a Edo
Waɗanda ke zanga-zanga a Edo na dauke da kwalaye masu rubutu daban-daban kamar, “A kawo ƙarshen tsadar rayuwa”, “FG ta kawar da yunwa a Najeriya yanzu,” da dai sauransu domin bayyana kokensu.
Ɗan takarar gwamna na New Nigeria Peoples Party (NNPP) a zaben watan Satumba na 2024, Dakta Azemhe Azena na cikin masu zanga-zangar a jihar Edo.
Sun kuma yi kira ga gwamnati da ta duba matsalolin da suka haifar da tsadar rayuwa tare da shawo kansu.
Meke faruwa a jihar Osun?
Haka lamarin ya kasance a Osogbo inda masu zanga-zangar suka taru a wurin shakatawa na Nelson Mandela da ke babban birnin jihar Osun, Punch ta rahoto.
Sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da ta kawo "ƙarshen tsadar rayuwa".
Zanga-zangar ta ranar Litinin ita ce ta baya-bayan nan a jerirn zanga-zanga kan tsadar rayuwa da ake ci gaba da yi a sassa daban-daban a Najeriya.
Zanga-zanga ta shiga jihar shugaban ƙasa
A wani rahoton kun ji cewa Da safiyar yau Litinin ce 26 ga watan Faburairu aka barke da zanga-zanga a jihar Legas kan halin da ake ciki a kasar.
Zanga-zangar na zuwa ne bayan gargadin da kwamishinan 'yan sanda a jihar ya yi a jiya Lahadi 25 ga watan Faburairu.
Asali: Legit.ng