NLC Ta Yi Bazaranar Ɗaukar Mataki 1 Idan Aka Farmaki Masu Zanga-Zangar Lumana a Ƙasar

NLC Ta Yi Bazaranar Ɗaukar Mataki 1 Idan Aka Farmaki Masu Zanga-Zangar Lumana a Ƙasar

  • Kungiyar kwadago ta yi barazanar cewa za ta rufe Najeriya baki daya ta hanyar janye ayyukan da ma'aikata ke yi idan aka kai mata hari
  • NLC ta yi zargin cewa akwai shirin da ake yi na farmakar 'yan kungiyar a yayin da suke gudanar da zanga-zangar lumana daga gobe Talata
  • Duk da samun matsin lamba na kar kungiyar ta gudanar da zanga-zangar, Joe Ajaero ya ce ba gudu babu ja da baya kan wannan kudiri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta yi wa gwamnati barazanar cewa za ta janye dukkan ayyukanta a duk fadin kasar.

NLC za ta dauki matakin ne idan har aka kai wa ‘yan kwadago hari a yayin gudanar da zanga-zangar kwanaki biyu da ta shirya daga ranar 27 ga Fabrairu, 2024.

Kara karanta wannan

‘Yan kwadago sun yanke matsaya kan hakura da zanga-zanga saboda barazanar DSS

NLC ta yi zargin cewa ana shirin kai masu hari idan suka fara zanga-zanga.
NLC ta yi zargin cewa ana shirin kai masu hari idan suka fara zanga-zanga. Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Twitter

Kungiyar kwadagon, a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, dauke da sa hannun shugabanta, Joe Ajaero, ta ce babu gudu babu ja da baya kan zanga-zangar da ta shirya, rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC za ta gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa

Ajaero ya ce tilas ne gwamnatin tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar da ta kulla da kungiyar kwadago tare da magance tabarbarewar tattalin arziki a Najeriya.

Najeriya dai na fama da hauhawar farashin kayayyaki, tsadar abinci, matsalar hada-hadar kudi, matsalar tattalin arziki da tsadar rayuwa sakamakon cire tallafin man fetur.

Duk da matsin lamba da gwamnati ke yi wa kungiyar na ka da ta fara zanga-zangar, NLC ta ce ba gudu ba ja da baya a wannan zanga-zangar da suke yi a fadin kasar.

Joe Ajaero ya gargadi gwamnati kan yunkurin kai masu hari

Kara karanta wannan

Dakarun noma: Gwamnati ta dauki mataki 1 na tsare manoma daga farmakin 'yan bindiga

Premium Times ta ruwaito kungiyar kwadagon ta kuma yi ikirarin cewa ta gano ana shirye-shiryen kai hare-hare kan masu zanga-zangar lumana afadin kasar.

Ajaero ya ce:

"Za mu so gwamnati ta sani cewa farmakar masu zanga-zangar lumana ba shi ne mafita ga mummunan halin da muke ciki na tattalin arziki da yunwa ba.
“Da wannan, mu a NLC da sauran kungiyoyin farar hula za mu ci gaba da gudanar da zanga-zangar mu na nuna rashin amincewa da tabarbarewar tattalin arziki da rashin tsaro.
"Za a tafka babban kuskure idan har aka kai mana hari domin zamu rufe baki daya Najeriyar ta hanyar janye ayyukan da ma’aikata ke yi."

Kungiyoyin farar hula 65 sun janye daga zanga-zagar NLC

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa akwai wasu kungiyoyi 65 na fararen hula da suka ce sun cire hannunsu a zanga-zagar da kungiyar kwadago ta ce za ta fara daga gobe.

Kungiyoyin sun fita daga kudirin NLC da cewar zanga-zagar na iya haifar da tashin hankula da kara jefa 'yan Najeriya a cikin wani mawuyacin halin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.