“Kada Wani Ya Damfare Ku”: NDLEA Ta Yi Ƙarin Haske Kan Rahoton Fara Ɗaukar Sabbin Ma’aikata

“Kada Wani Ya Damfare Ku”: NDLEA Ta Yi Ƙarin Haske Kan Rahoton Fara Ɗaukar Sabbin Ma’aikata

  • Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA, ta ja hankalin ‘yan kasar game da wani 'labarin karya' da ke yawo a shafukan sada zumunta
  • NDLEA ta ce labarin da ake yadawa cewa hukumar ta bude guraben aiki ga wadanda suka kammala jami'a da sakandare ba gaskiya ba ne
  • Hukumar ta jaddada cewa za ta sanar da daukar ma'aikata ne kawai a shafinta na yanar gizo da shafukan sada zumunta a lokacin da ya dace

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta yi wa jama’a karin haske game da ayyukan ‘yan damfara da ke yaudarar masu neman aiki a kasar.

Kara karanta wannan

Bayan jami'an sun kashe shugabannin 'yan bindiga, tsageru sun afkawa mutane a Kaduna

NDLEA, a wata sanarwa da Legit Hausa ta gani a baya-bayan nan, ta ce wasu miyagu na yaudarar mutane da sunan hukumar ta bude damar daukar aiki.

NDLEA ta gargadi jama'a game da ayyukan 'yan damfara.
NDLEA ta gargadi jama'a game da ayyukan 'yan damfara. Hoto: Stefan Heunis, AFP
Asali: Getty Images

Hukumar ta fusata kan ayyukan ‘yan damfara, inda ta kara da cewa a ko da yaushe mutane su rika neman haske daga masu rike da madafun iko kafin su nemi wani aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da gaske NDLEA ta bude kofar daukar sabbin ma'aikata?

Bugu da ƙari kuma, ta ce ba ta da wasu wakilai da ke taimaka mata wajen daukar ma'aikata.

NDLEA ta rubuta a kan shafinta na X (wanda aka fi sani da Twitter):

"Shirin damfara, ayi hattara!
"Ku yi watsi da duk wani labari da ke yawo na cewa hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA a halin yanzu na daukar ma'aikata.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa ake ci gaba da ganina a fim bayan na yi aure - Jaruma Rahma MK

"Hukumar za ta sanar da bayani game da daukar ma'aikata ne kawai a shafinta na yanar gizo: http://ndlea.gov.ng da kuma kafofin sadarwar mu @ndlea_nigeria akan YouTube, WhatsApp, Twitter da @ndlea01 akan Facebook."

Shafin NDLEA ya cunkushe saboda yawan masu neman aiki

A watan Maris, 2023, Legit Hausa ta ruwaito yadda shafin hukumar NDLEA ya gamu da cikas a daidai lokacin da hukumar ta sanar da daukar sabbin ma'aikata.

Saboda yawan ƴan Najeriya da suke kokarin cike bayanan neman aikin, shafin ya cunkushe tare da tsayawa cak!

Femi Babafemi, mai magana da yawun hukumar na wancan lokaci ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Litinin, 13 ga watan Maris, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.