An Bayyana Wadanda Suka Zuga Tinubu Ya Tafka Babban Kuskure Kan Rikicin Nijar

An Bayyana Wadanda Suka Zuga Tinubu Ya Tafka Babban Kuskure Kan Rikicin Nijar

  • Dr. Usman Bugaje ya yi magana kan yadda Shugaba Tinubu ya tunkari juyin mulkin da aka yi a Nijar
  • Tsohon ɗan majalisar wakilan ya bayyana cewa 'Lagos boys' ne suka ba Tinubu gurguwar shawara kan rikicin
  • Ya yi nuni da cewa matakan da aka ɗauka kan Jamhuriyar Nijar sun wuce hurumin ƙungiyar ECOWAS

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon dan majalisar wakilai, Dr Usman Bugaje, ya yi magana kan rikicin juyin mulkin Nijar da yadda aka ba Shugaba Tinubu shawara mara kyau.

Bugaje ya ce wasu na hannun daman shugaban ƙasa Bola Tinubu da suka yi aiki tare da shi lokacin yana gwamnan Legas sun ɓatar da shi kan rikicin juyin mulkin.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama ɗaliban fitacciyar jami'ar Arewa bisa zargin kashe rayukan bayin Allah

Bugaje ya caccaki Tinubu
Bugaje ya ce an ba Tinubu gurguwar shawara kan rikicin Nijar Hoto: Usman Bugaje/@KennedyWandera
Asali: Facebook

Wasu daga cikin na hannun daman Tinubu daga Legas waɗanda ke fadar shugaban ƙasa ana yi musu da laƙabi da 'Lagos boys'.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bugaje, wanda ya wakilci mazaɓar Kaita/Jibia ta jihar Katsina daga shekarar 2003 zuwa 2007 ya ce 'Lagos boys' sun nuna girman kai kuma sun kasa tuntuɓar masana kafin su shawarci Tinubu ya yi wa Nijar barazana bayan juyin mulkin.

Idan za a iya tunawa ƙasar Nijar da ke makwabtaka da Najeriya ta fuskanci juyin mulkin da ya hamɓarar da Shugaba Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli, 2023.

Me Bugaje ya ce kan rikicin Nijar?

Da yake magana kan yadda gwamnatin Najeriya ta tunkari rikicin Nijar, Bugaje wanda bai daɗe da dawowa daga Nijar ba, ya ce Tinubu ya yi abin da ya wuce hurumin ƙungiyar ECOWAS.

Bugaje, tsohon shugaban kwamitin harkokin ƙasashen waje na majalisar wakilai ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da gidan talabijin na Trust tv.

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnatin Tinubu ta shirya rabon tallafin N25,000 ga 'yan Najeriya

"Kafofin sada zumunta sun ce ‘Lagos boys' sun san komai. To, wataƙila wannan shi ne girman kai da suka zo da shi. Suna tunani kuma ba sa shawara a kan ko menene.
"Ina so mu ga cewa a matsayinmu na ƙasa mun keta ƙa'ida, mun yi abubuwan da suka wuce hurumin ECOWAS, kuma hakan ya haifar da munanan maganganu daga Nijar."

ECOWAS Ta Ɗage Takunkumin Nijar

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS) ta ɗage takunkumin da ta ƙaƙabawa Nijar.

Ƙungiyar ta ECOWAS ta ɗage takunkumin ne guda takwas wanda aka sanya biyo bayan juyin mulkin da aka yi a Nijar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng