Babban Abin Kunya: An Kama Matashi da Laifin Sace Motar Surukinsa, Ya Siyar N230,000
- Rahoton da muke samu ya bayyana yadda aka kama wani matashi da zargin sace motar surukinsa a Ogun
- An ruwaito cewa, tuni ya shiga hannun jami’an tsaro, kuma ya yi kokarin ba da cin hanci don a sake shi
- Ba wannan ne karon farko da ake kame matasa da aikata munanan ayyukan laifi na sata ba, hakan ya sha faruwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Jihar Ogun - An kama wani matashi dan shekara 27 mai suna Fatai Sholola da laifin satar mota mallakin mijin ‘yar uwarsa tare da siyar da ita akan kudi Naira 230,000.
Wasu jami’an So-Safe Corps ne suka kama Sholola a Sango ta karamar hukumar Ado-Odo/Ota ta jihar Ogun.
Kakakin So-Safe, Moruf Yusuf, ya tabbatar wa wakilin jaridar Punch kamen matashin a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaushe aka kama matashin da laifin sace mota?
A cewar Yusuf, sun kama Sholola da misalin karfe 2:00 na safe yayin da jami’an rundunar ke sintiri a kusa da Sango Plaza a ranar Juma’a.
Yusuf ya naqalto kwamandan So-Safe na jihar yana cewa:
“’Yan sintiri sun binciki jakar da yake rike da ita, kuma sun ga takardun mota a hannunsa, amma ya kasa bayyana dalilin da ya sa yake dauke da wadannan takardu.”
An ce wanda ake zargin ya yi yunkurin bai wa jami’an cin hancin Naira 30,000, amma suka ki amincewa, Osun Defender ta ruwaito.
Dama ana neman matashin ruwa a jallo kan sata
Ya kara da cewa:
“Abin takaici bayan titsiye shi an gano ya saci mota ne kuma takardun da ke hannunsa na motar da ya sace ne.”
An kuma ruwaito cewa, tuni an alanta neman wanda ake zargin ruwa a jallo tun kwanaki sama da takwas da suka gabata.
A halin da ake ciki dai ana ci gaba da bincike kan tushen lamarin tare da daukar matakin da ya dace na doka.
Majinyaci ya saci motar asibiti a Kano
A wani rahotonmu na baya, kun ji yadda wani majinyaci ya tattaro karfinsa ya sace motar asibiti a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya.
Wannan lamari dai ya faru ne da wani mutumin da ke jinyar karayar kafa a wani asibitin da ke birnin mai cunkoson jama'a.
Daga baya, an bayyana yadda 'yan sanda suka kama mutumin a karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa mai makwabtaka da Kano.
Asali: Legit.ng