Babbar Magana: Sunday Igboho Ya Zargi Buhari da Kisan Mahaifiyarsa da Kanwarsa, Bayanai Sun Fito
- An zargi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da kisan mahaifiya da kuma kanwar Sundy Igboho mai fafutukar kasar Yarbawa
- Igboho shi ya yi wannan zargi a yau Asabar 24 ga watan Faburairu a garin Igboho da ke jihar Oyo bayan ya kai ziyara
- Ya ce tsohon shugaban kasa, Buhari ne sanadin kisan mahaifiyar tasa inda ya zargi cewa ya yi yunkurin ganin bayansa shi ma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Oyo - Mai fafutukar kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho ya zargi tsohon shugaban kasa da kashe mahaifiyarsa da kuma kanwarsa.
Igboho ya ce tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne sanadin kisan mahaifiyar tasa inda ya zargi cewa ya yi yunkurin ganin bayansa shi ma.
Menene Igboho ke zargin Buhari?
Igboho ya bayyana haka ne a yau Asabar 24 ga watan Faburairu yayin ziyara a kauyen Igboho da ke jihar Oyo, cewar AbatiTV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya zargi cewa Buhari ya yi amfani da hukumar DSS da sojoji don ganin bayansa wanda suka zo har gidansa, cewar Vanguard.
Sunday wanda ya yi magana da Yarbanci ya ce ya kamata Kudu maso Yamma su hada kai don tsira daga kangin Fulani masu dauke da makamai.
Ya yi martani kan Fulani
A cewarsa:
“Buhari ya jawo matsaloli a rayuwata, ya hallaka kanwata da abokina da kuma mahaifiyata.
“Tabbas zai yi mutuwar abin mamaki da ‘ya’yansa, Buhari Fulani ne, mu ya kamata mu kula sosai da sosai.
“Buhari ya tura jami’an DSS da sojoji don su kama ni a gida na saboda na ce Yarbawa ba bayin Fulani ba ne, ba za su ci mu da yaki a garinmu ba.”
Har ila yau, Igboho ya kara da cewa Fulani ba za su iya hana iyayenmu zuwa gona ba, amma yanzu na dawo da karfin Ubangiji ba na dan Adam ba.
Igboho ya yi martani ga Sultan
Kun ji cewa mai fafutukar kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho ya yi martani ga Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar kan tsaro.
Igboho ya ce bai kamata a daurawa Tinubu laifin rashin tsaro da halin da ake ciki ba tun da shi ma gada ya yi a wurin Buhari.
Asali: Legit.ng