Shugaba Tinubu Ya Gamu da Sabuwar Matsala, ASUU Zata Sa Ƙafar Wando Ɗaya da FG Kan Muhimmin Abu 1

Shugaba Tinubu Ya Gamu da Sabuwar Matsala, ASUU Zata Sa Ƙafar Wando Ɗaya da FG Kan Muhimmin Abu 1

  • ASUU ta bayyana cewa za ta sa kafar wando ɗaya da gwamnatin tarayya karkashin shugaban ƙasa, Bola Tinubu, kan tsadar rayuwa
  • An shiga yanayin wahala da tsadar rayuwa sakamakon gyaran da Shugaba Tinubu ya ce ya fara kamar cire tallafin man fetur
  • Sai dai kungiyar ASUU ta ce ba wai a kan lamarin da ya shafi malaman jami'o'i kaɗai take ɗaukar mataki ba, harda halin da ƴan kasa ke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jos - Ƙungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa (ASUU) ta lashi takobin sa ƙafar wando ɗaya da gwamnatin tarayya kan halin matsin tattalin arzikin da al'umma suka shiga.

Wannan na zuwa ne yayin da ƴan Najeriya ke ji a jika sakamakon gyaran da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi iƙirarin yana yi a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnatin Tinubu ta shirya rabon tallafin N25,000 ga 'yan Najeriya

ASUU za ta sa kafar wando ɗaya da FG.
ASUU Ta Shirya Sa Kafar Wando Daya da Gwamnatin Tinubu Kan Tsadar Rayuwa Hoto: Bola Ahmed Tinubu, ASUU
Asali: Twitter

Koditen ASUU na reshen jihar Bauchi, Farfesa Nanmwa Voncir, ya ce ƙungiyar ta shirya yakar FG kan halin da ake ciki, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana haka ne ranar Jumu'a, 23 ga watan Fabrairu yayin zantawa da manema labarai a sakateriyar ASUU da ke Jos, babban birnin jihar Filato.

Wane hali ƴan Najeriya suka shiga?

Tun da ya karɓi mulkin Najeriya a shekarar da ta wuce, Tinubu ya dakatar da biyan tallafin man fetur da kula da kuɗaɗen waje.

Waɗannan matakai dai sun zama silar tashin farashin litar man fetur da hauhawar farashin kayan abinci da ya kawo tsadar rayuwa yayin da darajar Naira ta faɗi kan dala.

‘Yan Najeriya da dama sun fito kan tituna domin bayyana rashin jin dadinsu da salon shugabancin Tinubu duk da kiran da shugaban kasar ya yi na a ƙara hakuri.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Ƴan sanda sun bayyana mummunan laifin da ya sa aka kama shugaban LP na ƙasa

Wane mataki ASUU zata ɗauka kan taadar rayuwa?

Yayin hira da manema labarai, Voncir ya koka kan yanayin aiki a manyan makarantun kasar da kuma irin wahalhalun da ƴan Najeriya ke fuskanta.

A rahoton TVC News, Farfesa Voncir ya ce:

"Ba za mu taba jin tsoron tunkarar masu mulki a kasar nan ba matukar ba za su yi abin da ya dace ba. Ko a kan matsalar tattalin arzikin kasar nan, ASUU za ta tashi ta yaki gwamnati.
"Ba wai sai a kan aikin mu ba kawai, halin da ake ciki na matsin tattalin arzikin (da kuma) yadda talaka ke shan wahala, ASUU za ta tashi tsaye ta yi yaki.”

Jama'a sun daka wa notar abinci wawa a Katsina?

A wani rahoton kuma Hukumar ƴan sanda ta jihar Katsina ta fayyace gaskiya kan bidiyon da ke yawo na yadda mutane suka daka wa tirelar abinci wawa a jihar

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Aliyu, ya ce bincike ya nuna babu wani abu mai kama da haka da ya faru a kewayen Katsina

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262