Lauyoyin Murja Kunya Na Shirin Daukar Mataki 1 Tak Kan Gwamnatin Kano
- Lauyoyin jarumar TikTok da ke tsare, Murja Ibrahim Kunya, sun yi barazanar amfani da mataki na doka kan gwamnatin Kano
- Masu kare Murja, Aliyu Usman Hajji da Saddam Sulaiman, sun ba gwamnatin jihar sa'o'i 24 ta ba su damar ganin ta ko kuma su maka ta gaban alkali
- A cewarsu duk mutum da ake tuhuma yana da 'yancin ganin lauyoyinsa kamar yadda dokar kasa ta tanadar
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Jihar Kano - Har yanzu tsuguno bata kare ba kan lamarin fitacciyar jarumar TikTok, Murja Ibrahim Kunya wacce 'yan Hisbah suka kama tare da gurfanar da ita kan zargin yada badala.
A halin da ake ciki, lauyoyi masu kare 'yar TikTok din sun yi barazanar maka gwamnatin jihar Kano a kotu, idan har ba'a ba su damar ganinta ba cikin awanni 24.
Kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito, lauyoyin Murja, Aliyu Usman Hajji da Saddam Sulaiman, sun yi barazanar ne a cikin wata takarda da suka fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Su wa lauyoyin Murja suke barazanar makawa a kotu?
Sun dai kalubalanci matakin ci gaba da hana su ganin wacce suke karewa da gwamnatin jihar ta yi.
Wadanda lauyoyin suke zargin sun hana su yin ido hudu da wacce suke karewa sun hada da asibitin Muhammad Abdullahi Wase, wanda ke karkashin ikon hukumar asibitocin jihar Kano da na Hisbah.
Sauran wanda suke zargi shine magatakardar kotun Shari'ar Musulunci ta Kwana Hudu PRP.
Jaridar ta kuma rahoto cewa, Mai Shari’a Nura ne Yusuf ya bayar da izinin yi wa Murja Kunya gwajin kwakwalwa a asibitin gwamnatin domin tabbatar da cikar hankalinta.
An tattaro cewa alkalin ya bayar da umurnin ne kan zargi da ake na bata cikin hayyacinta a yayin da aka yi zaman farko a kotun.
Me lauyoyin Murja suka ce?
An nakalto lauyoyin jarumar suna cewa:
“A binciken da muka gudanar, wacce muke karewa ta yi biyayya ga umarnin kotu inda a yanzu haka takeAsibitin Nassarawa karkashin kulawarku.
"Sai dai kuma, a ranar 22 ga watan Fabrairu, mun bukaci ganin ta domin mu tattauna da ita, amma aka hana mu ganin ta, kuma hakan ya yi karo da kundin tsarin mulki na 1999 da aka yi wa gyara."
An rahoto cewa tuni takardar gargadin ta isa asibitin Nasarawa da hukumar Hisbah, inda wasu jami'an hukumomin suka sanya hannu a kai.
Kotu ta sake bada umurni kan Murja
A baya dai mun ji cewa kotun Shari'ar Musulunci a Kano ta sake ba da sabon umarni kan shari'ar 'yar Tiktok, Murja Ibrahim Kunya.
Kotun da ke zamanta a Gama PRP a jihar Kano ta umarci likitoci su duba lafiyar kwakwalwar Murja Kunya.
Asali: Legit.ng