Kwastam Ta Fara Raba Wa Talakawan Najeriya Kayan Abinci da Ta Kwace, Ta Fadi Ka'idojin Cin Gajiyar

Kwastam Ta Fara Raba Wa Talakawan Najeriya Kayan Abinci da Ta Kwace, Ta Fadi Ka'idojin Cin Gajiyar

  • Yayin da ake cikin mawuyacin halin tsadar rayuwa a Najeriya, hukumar Kwastam ta shirya raba kayan abinci da ta kwace
  • Shugaban Hukumar, Adewale Adeniyi shi ya bayyana haka a jiya Alhamis 22 ga watan Faburairu a jihar Legas
  • Adeniyi ya ce za su fara raba kayan abincin da suka kwace a hannun wasu a yau Juma'a 23 ga watan Faburairu a fadin kasar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kwanturolan hukumar Kwastam, Adewale Adeniyi ya tabbatar da cewa za a fara rabon kayan abinci a yau a jihar Legas.

Adeniyi ya na magana ne kan abincin da suka kwace daga hannun wadanda ake zargin su da fitar da abincin waje.

Kara karanta wannan

Mutum 1 ya mutu yayin da aka kaure tsakanin Hausawa da Yarbawa a Legas, bayanai sun fito

Kwastam ta fara raba abinci a Najeriya yayin da ake cikin yanayi
Hukumar Kwastam ta fara raba kayan abinci da ta kwace a yau Juma'a. Hoto: Nigeria Custom Service.
Asali: Twitter

Yaushe Kwastam ta fara raba kayan abincin?

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban hukumar ya bayyana haka ne a jiya Alhamis 22 ga watan Faburairu a birnin Legas, Vanguard ta tattaro.

Ya gargadi jami'an hukumar da aka haramta musu shiga aikin kwace abincin wurin sake siyar da shinkafar.

Ya ce daga cikin kayan akwai shinkafa mai nauyin kilo 25 wanda za a siyar da ita na'ura dubu 10 kacal.

Yadda Kwastam za ta yi tsarin rabon kayan abincin

Yayin da ya ke ba da bahasi kan tsarin rabiyar, Adeniyi ya ce duk wanda ke son cin gajiyar sai ya nuna shaidar lambar NIN, Nairametrics ta tattaro.

Ya ce wadanda za su ci gajiyar sun hada da masu sana'ar hannu da malaman makaranta da nas-nas da kungiyoyin addinai sa sauran 'yan Najeriya.

Wannan na zuwa ne yayin da hukumar ke zargin wasu 'yan kasuwar da fitar da kayan abinci yayin da 'yan kasar ke cikin mawuyacin hali.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Babbar matsalar Tinubu gwamnoni ne, kungiya ta fadi abin da gwamnonin ke yi a boye

Sarkin Kano ya shawarci hukumar Kwastam

A baya, mun baku labarin cewa Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya shawarci Hukumar Kwastam kan irin taba 'yan kasuwa da ta ke da yi.

Sarkin ya ce ya kamata hukumar ta bar 'yan kasuwar su sarara idan har ba su saba ka'ida ba na dokokin hukumar.

Hakan na zuwa ne yayin da hukumar ke zargin wasu 'yan kasuwar da fitar da kayan abinci yayin da 'yan kasar ke cikin mawuyacin hali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.