Labari Mai Daɗi: Farashin Dala Zai Faɗi Warwas a Najeriya Nan Ba da Daɗewa Ba, Gwamna Ya Magantu
- Dapo Abiodun ya tabbatar da cewa nan da wani taƙaitaccen lokaci dala zata rikito ta faɗo ƙasa yayin darajar Naira za ta dawo a Najeriya
- Gwamnan ya bayyana cewa ya samu wannan tabbaci ne a wurin ganawar da gwamnoni suka yi da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu
- Ya kuma sanar da cewa gwamnatinsa ta siyo tirelolin shinkafa kusan 100 da za a rabawa tsofaffi da marasa ƙarfi a faɗin jihar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ogun - Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya bayyana cewa nan da wata ɗaya tal mai zuwa, dala za ta rikito ƙasa ta koma karkashin Naira a Najeriya.
Abidoun ya faɗi haka ne a wurin taron masu ruwa da tsaki wanda ya gudana a cibiyar al'adu da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun kan matsin tattalin arzikin da ake ciki.
Gwamnan ya ce ya samu wannan tabbacin ce a wurin taron gaggawa da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi da gwamnonin jihohin ƙasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce Gwamnatin Tarayya tana sane da kalubalen da ake fuskanta kuma a shirye take ta magance matsalar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
"Ina mai tabbatar muku da cewa dala za ta fadi kasa nan da wata guda. Mun samu tabbaci a ganawar da muka yi da shugaban kasa.
"Kuma muna da masaniyar cewa akwai masu zagon kasa ga tattalin arzikin ƙasar nan, amma burinsu ba zai yi nasara ba."
Wane mataki gwamnati ke ɗauka na sauƙaƙa wa talakawa?
Dangane da matakan da gwamnatinsa ta ɗauka, Gwamna Abiodun ya ce zai samar da kayan abinci kamar su Shinkafa, gari da wake ga mazauna jihar.
Ya ci gaba da cewa
"Na shirya kawo tireloli kusan 100 na shinkafa, kuma za a fara sauke su daga gobe. Domin a yi adalci, zamu rabawa tsofaffi da masu karamin ƙarfi kyauta, saura kuma zasu siya kan farashin kafin tashin dala."
Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta tsara shirin tallafi wanda za a raba Shinkafa da sauran kayan abinci ga magidanta 300,000 a faɗin jihar Ogun, Daily Post ta rahoto
Gwamnan Legas ya waiwayi ma'aikata
A wani rahoton kuma Babajide Sanwo-Olu ya sanar da matakan da gwamnatinsa ta ɗauka domin rage wa mazauna jihar Legas raɗaɗin halin matsin da aka shiga.
Gwamnan ya bayyana rage wa ma'aikata ranakun aiki daga kwanaki 5 zuwa 3, yayin da malamai kuma za a ba su alawus na hawa mota.
Asali: Legit.ng