Kano: Yayin da Ake Tunkarar Watan Ramadan, Gwamna Abba Kabir Ya Dauki Muhimmin Mataki Kan Azumin
- Yayin da ake tunkarar azumin watan Ramadan, Gwamna Abba Kabir ya kafa kwamiti don saukakawa jama'a
- Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam yayin kaddamar da kwamitin ya ce an kafa kwamitin ne don ciyar da jama'a
- Wannan na zuwa ne yayin da mutane su ke cikin mawuyacin halin tsadar rayuwa a kasar baki daya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Yayin da ake tunkarar watan Ramadan, Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin don ciyar da mutane.
Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam shi ya kaddamar da kwamitin a jiya Laraba 21 ga watan Faburairu a jihar Kano.
Dalilin kafa kwamitin da ka yi a Kano
Aminu ya ce an samar da shirin ne don taimakawa ‘yan jihar ba tare da nuna bambancin siyasa ba, cewar Daily Nigerian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bukaci kwamitin da su samo hanyar rarraba abincin a duk fadin jihar inda ya nuna amfanin kammala hakan a cikin kwanaki biyar.
Ya kuma bukaci sabunta tsohon rahoton da aka gudanar a baya don tabbatar da gyara dukkan kura-kuran da ke ciki.
Mataimakin gwamnan ya ce daga cikin abin da ake bukata akwai samar da wuraren rabiyar a dukkan kananan hukumomi 44 a jihar.
Martanin kwamishina kan wannan aiki
A cewarsa:
“Kwamitin ya kuma samar da ba da abincin sahur ga al’ummar Musulmai a lokacin Ramadan musamman wandanda suka cancaki hakan.”
Aminu ya godewa al’ummar jihar Kano saboda irin goyon baya da suke bai wa Gwamna Abba Kabir, cewar PM News.
Bayan yunwa ta nakasa mutane, Gwamna a Arewa ya sake fitar da shinkafa don marasa karfi, an bi tsari
A martaninsa, kwamishinonin harkokin Addinai, Ahmad Auwal ya godewa gwamnatin jihar da irin wannan aiki da suka daura musu.
Sauran wadanda suke cikin kwamitin sun hada da kwamishinonin ma'aikatun harkokin mata da ayyuka na musamman da ilimi da kuma yada labarai.
An kai karar Sunusi Lamido wurin Tinubu
Kun ji cewa wata kungiya ta kai kara tsohon Sarkin Kano, Sunusi Lamido Sunusi wurin Shugaba Bola Tinubu.
Kungiyar ta ce ya kamata Shugaba Tinubu ya takawa Lamido birki kan irin kalamansa da mukarrabansa da ka iya jawo rashin zaman lafiya.
Asali: Legit.ng