Wani ‘Dan Najeriya Ya Bankado Wani Boyayyen Sirri Na Matarsa Mai Juna Biyu

Wani ‘Dan Najeriya Ya Bankado Wani Boyayyen Sirri Na Matarsa Mai Juna Biyu

  • Wata matashiya 'yar Najeriya ta bada labarin yadda mijinta ya yi bayan ya gano cewa kudin awon ciki N5k ne kacal
  • Matar mai juna biyu ta fallasa a TikTok cewa N50k take ta karba daga wajensa a matsayin kudin awon ciki
  • Mutanen da suka kalli bidiyon sun garzaya sashin sharhi don tuna yanayin yadda nasu awon cikin ya gudana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Mijin wata 'yar Najeriya mai dauke da juna biyu ya kama ta tana yi masa yankan aljihu da sunan kudin awon ciki.

Matashiyar mai suna @presh4521 a dandalin TikTok ta bayyana a wallafarta cewa ta dade tana kara kudin awon ciki.

Miji ya gano kudin awon ciki 5k ne ba 50k ba
Wani ‘Dan Najeriya Ya Bankado Wani Boyayyen Sirri Na Matarsa Mai Juna Biyu Hoto: @presh_xoxo/TikTok
Asali: TikTok

Matashiya na karbar N50k kudin awon ciki

A cewarta, ta dade tana karbar N50k daga wajen mijinta a matsayin kudin awon ciki.

Kara karanta wannan

Tinubu yana bakin kokarinsa, ana yunwa a sauran kasashen waje Inji Sanatan APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, mutumin mai matukar wayo ya gano cewa kudin da asibitin ke karba na awon ciki N5,000 ne kacal.

Wani bidiyo mai ban dariya ya nuno yadda matar da durkusa a gaban mijin nata don ta roke shi bayan ta gano cewa ta dade tana yi masa karya.

"POV: mijina ya gano cewa kudin awon ciki ba 50k bane face 5k," taken da ta yi wa bidiyon.

Jama'a sun yi martani yayin da miji ya gano karyar matarsa

@dorabeauty ta yi martani:

"Mijina ya kira surukata da take malamar jinya sannan ya tambayeta nawa ne kudin awo sai ta ce duk abin da matarka ta fada maka gaskiya ne."

Mim ta yi martani:

"Toh idan ya zamana mijinka likita ne mai mutum zai yi don Allah ku taimaki 'yar'uwa."

@joy ta ce:

Kara karanta wannan

Sanata Sani ya fadi mafita 1 da Musulmi da Kiristoci zasu runguma domin farfado da naira

"Allah ya yafe mani don na karba ya fi miliyan 2."

Qwinkaldre ta ce:

"Allah ka taimaki mijina saboda zai sha wahala."

SPECIAL GODSPOWER ta ce:

"2ok nake karba."

Nonos_Signatureta yi martani:

"Nawa 40k ne asibitin kudi."

Mota ta kade mai juna biyu

A wani labarin, mun ji cewa wata babbar mota ta murkushe mata mai ciki da raunata yaronta mai shekaru biyu a karamar hukumar Obafemi Owode da ke jihar Ogun.

Punch ta tattaro cewa direban motar ya gagara shawo kan motar bayan birki ya balle inda ya kutsa cikin kasuwa, Legit.ng ta tattaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng