Majalisar Dattawa Ta Amince da Wasu Muhimman Nade-Nade da Shugaba Tinubu Ya Yi
- Majalisar dattawa ta amince da naɗin shugabannin hukumomin NAHCON da NHIA wanda Shugaba Tinubu ya yi
- Majalisar ta amince da naɗin Dr Kelechi Ohiri a matsayin darakta janar na hukumar NHIA mai kula da inshorar lafiya
- Majalisar ta kuma amince da naɗin Malam Jalal Arabi da kwamishinonin hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON)
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Majalisar dattawa a ranar Laraba ta tabbatar da sunayen mutanen da Shugaba Bola Tinubu ya naɗa a matsayin shugaba da mambobin hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON).
Majalisar dattawan ta kuma tabbatar da sunan wanda Shugaba Tinubu ya naɗa don zama darakta janar na hukumar inshorar lafiya ta ƙasa (NHIA), cewar rahoton jaridar Daily Trust.
An tabbatar da waɗanda aka naɗa ne bayan gabatarwa tare da la'akari da rahotannin kwamitocin majalisar dattawa kan harkokin kiwon lafiya da harkokin ƙasashen waje.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tabbatar da Dr Kelechi Ohiri a matsayin Darakta Janar na hukumar NHIA.
Waɗanda aka tabbatar daga hukumar NAHCON sun haɗa da, Malam Jalal Arabi a matsayin shugaba, Aliu AbdulRazak, kwamishinan ma'aikata da kuɗi, Prince Anofiu Elegushi, kwamishinan ayyuka.
Na ƙarshe daga ciki shine Farfesa Abubakar Yagawal, kwamishinan tsare-tsare da bincike.
Jaridar Independent ta ce shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya buƙaci sabbin waɗanda aka naɗa muƙaman da su tabbatar da cewa kwalliya ya biya kuɗin sabulu kan naɗin na su ta hanyar gudanar da ayyukansu da kyau.
Majalisar dattawa ta tabbatar da kwamishinonin NPC
Legit Hausa ta kawo rahoto cewa majalisar dattawa ta amince da naɗin kwamishinoni 17 na hukumar ƙidaya ta ƙasa (NPC), bayan ta kammala tantance su.
Amincewa da naɗin na su ya biyo bayan aikewa da sunayensu da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi zuwa gaban majalisar a watan Disamban 2023.
Majalisar Dattawa Ta Tabbatar da Naɗin Shugaban NMDGIFB
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawa ta tabbatar da naɗin sabon babban darakta na hukumar kula da ayyukan samar da iskar gas ta Najeriya (NMDGIFB).
Majalisar dattawan ta amince da naɗin Adama Oluwole Oladapo, a matsayin sabon daraktan hukumar bayan Shugaba Tinubu ya aike mata da wasiƙar neman ta amince da naɗin nasa
Asali: Legit.ng