An Shiga Mummunan Yanayi Bayan Mata Ta Tunkudo Mijinta Daga Saman Bene Kan Wani Dalili, Ya Rasu
- Rashin tausayi kullum karuwa ya ke yi ta bangaren mata yayin ta wata ta tunkudo mijinta daga saman bene a jihar Ebonyi
- Matar ta aikata hakan ne yayin da suke jayayya da mijin nata kan rikicin iyali saboda mijin ya na auren mata biyu
- Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, DSP Ukanda Joshua ya ce har zuwa wannan lokaci bai samu rahoton lamarin ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ebonyi – An shiga tashin hankali bayan wata mata ta tunkudo mijinta daga saman bene mai hawa biyu a jihar Ebonyi.
Lamarin ya faru ne a safiyar ranar Talata 20 ga watan Faburairu inda matar mai dauke da juna biyu ta hallaka mijin nata, cewar Punch.
Me ake zargin matar da aikatawa?
Marigayin Nwoga Maduabuchi wanda dan asalin kauyen Akpata ne da ke karamar hukumar Izzi ya auri matar ce a matsayin ta biyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani jami’in tsaro da ya bukaci boye sunansa ya tabbatar da cewa marigayin na jayayya da matar ce kan matsalar iyalinsu lokacin da abin ya faru.
Majiyar ta ce:
“Mutumin kawai ya gamu da tsautsayin matsalar iyali ne wanda ya ke tare da matansa guda biyu da ya auro.
“Rikicin iyalai ne ya jawo, amma mata ta biyun ta fusata inda ta aikata hakan wanda yin hakan karshen rashin imani ne.”
Martanin 'yan sanda kan lamarin
Wata majiya har ila yau, ta tabbatar da cewa matar ta na dauke da juna biyu inda ake yawan zarginta da fitina, cewar BNN Breaking.
Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, DSP Ukanda Joshua ya ce har zuwa wannan lokaci bai samu rahoton lamarin ba daga jami’ansu.
Ukanda ya ce bai san ta ina abin ya faru a birnin Abakaliki ba bare ya iya sanin ainihin abin da ya jawo faruwar hakan.
Ya tambaya ta ina ne abin ya faru don ya tuntubi DPO na wannan yankin ko zai samu karin bayani, Pageone ta tattaro.
‘Yan sanda sun saki Abure
Kun ji labarin cewa rundunar yan sanda ta sake shugaban jam’iyyar adawa ta LP, Julius Abure kan zargin kisan kai.
Abure dai an kama shi ne da shugaban jam’iyyar jihar Edo da sakataren yada labaranta da kuma wasu mutane biyu.
Asali: Legit.ng