Awanni Kadan Bayan Cafke Shugaban Jam’iyyar Adawa a Najeriya, ’Yan Sanda Sun Dauki Mataki Kansa
- Bayan shafe awanni a ofishin ‘yan sanda, shugaban jam’iyyar LP ta kasa, Julius Abure ya samu damar fitowa daga kangin
- Rahotanni sun tabbatar da cewa an sake Abure ne da misalin karfe 3:00 na dare yau Alhamis 22 ga watan Faburairu
- Wannan na zuwa ne bayan cafke Abure a jiya Laraba ce 21 ga watan Faburairu da wasu mutane hudu kan zargin kisan kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Edo – Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da sakin shugaban jam’iyyar LP ta kasa, Julius Abure da aka kama.
A jiya Laraba ce 21 ga watan Faburairu mataimakin sifetan ‘yan sanda ya cafke Abure a Benin City kan zargin kisan kai.
Yaushe aka cafke Abure?
Tribune ta tabbatar da cewa an sake Abure ne da misalin karfe 3:00 na dare yau Alhamis 22 ga watan Faburairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
AIG Arungwa Nwazule a daren ranar Laraba 21 ga watan Faburairu ya ce sun cafke Abure da kuma shugaban jam’iyyar a jihar da wasu mutane uku kan zargin.
Da yake martani bayan sakin nasa, Abure ya ce shi ma ya gamu da irin jarabawar da sauran masu gwagwarmaya suke sha ne.
Abure ya ce sakin nasa ya na da nasaba da kiraye-kirayen da aka ta yiwa jami’an ‘yan sandan daga wasu bangarori, cewar TheCable.
Ya kuma yi alkawari ga shugaban jam’iyyar a jihar da sakataren yada labaran LP da sauran cewa nan ba da jimawa ba za a sake su.
Ya kara da cewa babu wani abu da zai kashe masa gwiwa wurin tabbatar da neman muradun jam’iyyarsa.
Martanin Abure bayan sake shi
A cewarsa:
“Ina matukar godiya ga wadanda suka nuna min goyon baya, babu wata gwagwarmaya da ta ke da sauki kowa ya sani.
“Tun bayan zabe suke ta neman kawo rikici a jam’iyyar da zarge-zarge kala-kala wanda daga bisani ‘yan sanda sun doru a kai kuma sun gane karya ce.
“Jiya muna kokarin zaben fidda gwani ‘yan sanda suka zo wurin tare da kama mu kan zargin da ba na son ambata saboda ana kan bincike yanzu haka.”
‘Yan sanda sun kama Abure
Kun ji cewa shugaban jam’iyyar LP ta kasa, Julius Abure ya shiga hannun ‘yan sanda bayan cafke shi da aka yi.
Ana zargin Abure da shugaban jam’iyyar a jihar Edo da wasu mutane uku kan zargin kisan kai.
Asali: Legit.ng