EFCC Ta Tara Hujjojin Zargin Satar N10bn, Za a Gurfanar da Tsohon Gwamna a Kotu
- Bisa dukkan alamu hukumar EFCC ta tara hujjojin da ta ke nema domin yin shari’a da Abdulfattah Ahmed a gaban kotu
- Wata majiya ta shaida a ranar Juma’ar nan mai zuwa tsohon gwamnan Kwara zai tsinci kan shi yana shari’a da gwamnati
- EFCC mai yaki da rashin gaskiya tana tuhumar Abdulfattah Ahmed da karkatar da biliyoyin kudi a lokacin da ya yi mulkinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya za ta gurfanar da Abdulfattah Ahmed a kotu bisa zargin da ake yi masa.
Idan rahoton Punch ya tabbata, a ranar Juma’ar nan mai zuwa EFCC za ta fara shari’a da Abdulfattah Ahmed a kotun tarayya.
Za a kai tsohon gwamnan Kwara kotu
Ana zargin tsohon gwamnan na jihar Kwara da laifin satar N10bn a lokacin yana ofis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya ta shaida cewa za a kai karar tsohon gwamnan ne a babban kotun tarayya da ke birnin Ilorin a jihar Kwara.
“A ranar Juma’a za a gurfanar da shi a kotun tarayya da ke Ilorin bisa zargin karkatar da dukiyar da ta kai N10bn”
- Majiya daga EFCC
Abdulfatah Ahmed v EFCC: An tsare tsohon gwamnan Kwara
Tun ranar Litinin ‘dan siyasar yake tsare a hannun hukumar EFCC, ana da labarin ya fara kokawa kan halin da ya tsinci kan shi.
Ahmed ya yi zargin an hana shi ganin likitoci, lauyoyi da kuma masu girka abinci.
Gayyatar hukumar EFCC ta canza salo
Alhaji AbdulWahab Oba wanda shi ne sakataren yada labaran tsohon gwamnan ya ce EFCC ta gayyace shi ne sai ya je ofishinta.
Daga baya ya tabbatar da cewa ziyarar ta canza salo domin jami’an hukumar sun rike shi bayan an yi tunanin abin bai kai haka ba.
Alhaji AbdulWahab Oba ya nuna ba su san laifin da ake tuhumar mai gidan na su ba, ya ce an kuma tsaurara sharudan bada belinsa.
An hana Ahmed sakat bayan barin ofis
A shekarun baya an ji labari hukumar AMCON ta karbe gidan Abdulfatah Ahmed bayan hukuncin da wani alkali ya yi a Legas.
'Yan jam’iyyar PDP na reshen Kwara suna ta zanga-zanga a Ilorin, su na ganin akwai siyasa a yadda aka taso jagoran na su a gaba.
Asali: Legit.ng