'Dan Majalisar Tarayya Ya Soke Bikin Zagayowar Ranar Haihuwarsa Saboda Tsadar Rayuwa
- Cike da damuwar halin da tattalin arziki ke ciki wanda ya haifar da yunwa a fadin kasar, Hon. Phili Agbese ya soke bikin zagayowar ranar haihuwarsa
- Dan majalisar ya ce matakin da ya dauka ya zama dole saboda yana tare da mutanen Najeriya a wannan mawuyacin lokaci da ake ciki
- Ya bayyana cewa a wannan lokaci ne da ya kamata a zurfafa tunani maimakon bukukuwan almubazzaranci da kece raini
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
FCT, Abuja - Cif Philip Agbese, 'dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Ado, Okpokwu, da Ogbadibo a jihar Benue, ya yanke shawarar soke shagalin bikin zagayowar ranar haihuwarsa da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Agbese ya yarda cewa duk da cewa ranar haihuwarsa wani muhimmin lokaci ne, dole a hakura da na bana saboda halin da ake ciki.
A cewar sanarwar:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ranar 25 ga watan Fabrairu rana ce ta musamman a gare ni, domin murnar zagayowar ranar haihuwata, a duk shekara ta kan ba ni damar yin tsokaci da kuma nuna godiya ga Allah saboda kyautar rayuwa da ya yi mani.
“Duk da cewa wannan abin farin ciki ne kuma da yawa suna son a yi shi cikin salo na kece raini, sai dai kuma, bikin bana ya zo da wani al'amari saboda matsi, wahala da kunci da ake ciki a kasar.
"Menene fa'idar yin biki na kece raini alhalin da kyar 'yan Najeriya ke cin abinci? Menene ma'anar jin dadi tare da manyan mutane yayin da wadanda suka zabe ni a matakin farko suna rayuwa cikin tsoro, yunwa da wahala?"
'Dan majalisar ya yarda 'yan Najeriya na shan wahala
Ya ambaci cewa yana ganin abu ne mai muhimmanci ya yi 'dan tsokaci kafin zagayowar ranar haihuwarsa.
'Dan siyasar ya nuna aniyarsa na son yin bikin zagowar ranar haihuwarsa a sawwake ta tare da wani kasaitaccen biki ba.
Ya jadadda cewar wannan lokaci ne na yin tunani mai tsanani fiye da bukukuwan kece raini.
Agbese ya ce:
"Saboda haka, ina so in yi kira ga abokaina, takwarorina da abokan tarayya ta da su bayar da kudadensu ga iyalansu, al'ummominsu, mazabunsu da kuma marasa karfi a cikinmu. Ku raba soyayyata tare da su."
Wani dattijo ya koka da tsadar rayuwa
A wani labarin, mun ji cewa al'ummar Najeriya na ci gaba da kokawa yayin da tsadar rayuwa da hauhawar farashin kaya ke kara kamari a kasar.
Kan haka ne wani dattijo ya fito dandalin soshiyal midiya domin yin zanga-zanga kan halin da ake ciki, ya kuma aika sako ga shugabanni kan halin da talaka ke ciki a Najeriya.
Asali: Legit.ng