Tsadar Rayuwa: Hukumar DSS Ta Gargadi Kungiyoyin Kwadago Kan Gudanar da Zanga-Zanga, Ta Fadi Dalili

Tsadar Rayuwa: Hukumar DSS Ta Gargadi Kungiyoyin Kwadago Kan Gudanar da Zanga-Zanga, Ta Fadi Dalili

  • An yi kira ga ƙungiyoyin ƙwadago da su ƙauracewa zanga-zangar da suka shirya yi a faɗin ƙasar nan domin samun zaman lafiya
  • Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta bayar da wannan gargadin ne bayan NLC ta ayyana zanga-zangar kwana biyu ta ƙasa a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairu
  • Kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya, ya ce rundunar ƴan sandan sirrin ta gano cewa wasu ɓata gari na shirin yin amfani da zanga-zangar don haifar da rikici

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta buƙaci ƙungiyoyin ƙwadago da su yi watsi da shirin gudanar da zanga-zanga a ranakun 27 zuwa 28 ga watan Fabrairun 2024 domin samar da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

'Yan kwadago sun jero sabbin sharuɗda ga Gwamnatin Tinubu kan tsadar rayuwa, bayanai sun fito

Kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a shafin X na hukumar @OfficialDSSNG, ranar Laraba, 21 ga watan Fabrairu.

DSS ta gargadi kungiyoyin kwadago
DSS ta bukaci kungiyoyin kwadago su hakura da zanga-zanga Hoto: DSS/@NLCHeadquarters
Asali: UGC

An tattaro cewa za a gudanar da zanga-zangar ne a sassan ƙasar nan kan taɓarɓarewar tattalin arziƙi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me yasa DSS ta yi gargaɗi kan zanga-zangar?

Afunanya ya buƙaci ƙungiyoyin ƙwadagon da su ci gaba da tattaunawa maimakon yin zanga-zangar da ka iya haifar da tashin hankali a ƙasa.

Ya bayyana cewa hukumar ta DSS ta gano cewa wasu ɓata gari na shirin yin amfani da zanga-zangar don tada rikici da kawo tashin hankali.

Kakakin na DSS ya ce ya kamata ƙungiyoyin ƙwadagon su ba gwamnati a kowane mataki lokaci domin suna ƙoƙarin ganin sun daidaita yanayin tattalin arzikin da ake ciki.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya bukaci ayi abu 1 don kawo karshen matsalar tsaro

“Hukumar DSS ta ƙara kira ga ɓangarorin da su ci gaba da tattaunawa maimakon yin wasu abubuwa da za su iya tada zaune tsaye.
"Hukumar tana sane da cewa wasu ɓata gari na shirin yin amfani da damar zanga-zangar don tada rikici da kuma tashe-tashen hankula.
"Zanga-zangar ba tare da wata shakka ba, za ta dagula al'amuran zamantakewa da tattalin arziki a faɗin ƙasar nan.
"Sanin kowa ne cewa dukkan matakan gwamnati suna ƙoƙari don inganta yanayin tattalin arzikin da ake fama da shi, don haka ya kamata a ƙara yi musu uzuri."

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Tsunduma Yajin Aiki

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ƙwadago a jihar Neja ta sanar da tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a faɗin jihar.

Ƙungiyar ƙwadagon ta ce ba za ta janye daga yajin aikin ba har sai gwamnati ta warware dukkan saɓanin da ke a tsakaninsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng