Yayin da Dokar ’Yan Sandan Jiha Ta Tsallake Karatu Na 2, an Fadi Dokar Nada Kwamishinonin ’Yan Sanda

Yayin da Dokar ’Yan Sandan Jiha Ta Tsallake Karatu Na 2, an Fadi Dokar Nada Kwamishinonin ’Yan Sanda

  • Kudirin samar da ‘yan sandan jihohi ya tsallake kararu na biyu yayin da dokar ta fayyace nada kwamishinonin ‘yan sanda
  • Dokar ta bai wa gwamnonin jihohi damar nada kwamishinonin ‘yan sanda a jihohinsu kamar yadda aka bayyana
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wani jami'in dan sanda kan wannan lamari na sabuwar dokar kirkirar 'yan sandan jihohi a Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Yayin da kudirin samar da ‘yan sandan jihohi ya tsallake karatu na biyu, an ba da sabon umarni kan zabar kwamishinan ‘yan sanda.

Sabuwar dokar da ke neman kirkirar ‘yan sandan jihohi an kawo ta ne saboda dakile matsalar tsaro da ya yi katutu a jihohi.

Kara karanta wannan

Yunwa: An ‘rabawa’ gwamnoni karin Naira Biliyan 30 kwanan nan, Shugaban Majalisa

An fayyace dokar nada kwamishinonin 'yan sanda da gwamnoni za su yi
Dokar na zuwa ne bayan kudirin ya tsallake karatu na biyu a Majalisa. Hoto: Nigeria Police Force, NGF.
Asali: Facebook

Mene dokar ke cewa kan 'yan sandan?

Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya gana da gwamnonin jihohi kan matsalar tsaron da ta addabe su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bangaren nada kwamishinan ‘yan sanda wanda gwamnan jiha zai yi, dokar ta fayyace cewa dole sai da amincewar Majalisar jihar.

Har ila yau, gwamnan ba zai iya nada kwamishinan ba har sai ya samu amincewa daga hukumar ‘yan sanda ta Tarayya.

Dadi da kari, gwamnan jiha zai iya cire kwamishinan ‘yan sanda da amincewar hukumar ‘yan sanda ta Tarayya da kuma amincewar kaso biyu cikin uku na Majalisar jiharsa.

Dokar ta bayyana cewa dole za a kirkiri hukumar ‘yan sanda ta jihohi da za ta rika sa ido a bangarorin aikin dan sanda, cewar Premium Times.

Karfin ikon gwamna kan kwamishinan 'yan sanda

Gwamnan jiha zai iya bai wa kwamishinan ‘yan sanda umarni karkashin doka amma idan ya saba doka kwamishinan zai iya kai kara zuwa hukumar ‘yan sandan jihar.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta shiga rudani bayan ayyana zaben fidda gwanin Edo 'Inconclusive', ta fadi dalili

Har ila yau, Majalisar Tarayya ce za ta rika sabunta kasancewar hukumar ‘yan sandan jihohi duk bayan shekaru biyu don tabbatar da su na kan tsarin doka.

Dokar ta kuma fayyace aikin dan sandan Gwamnatin Tarayya da na jiha musamman a wurin samar da zaman lafiya, cewar Daily Post.

Dokar ta kara da cewa ‘yan sandan Tarayya ba su da hurumin shiga harkokin tsaron jihar har sai gwamna ya bukaci haka ko kuma an samu tabarbarewar tsaro da ka iya jefa jihar cikin wani hali.

Legit Hausa ta ji ta bakin wani jami'in dan sanda kan wannan lamari.

Jami'in wanda ya bukaci a boye sunansa ya ce ya na tsoron a mayar da su saniyar ware a jihohin da ke fama da matsalolin tsaro.

Ya ce:

"Musamman ganin yadda dokar za ta bai wa gwamnoni daurawa da sauke kwamishinonin 'yan sanda tabbas za a samu matsala da mu da ke Gwamnatin Tarayya.

Kara karanta wannan

Yan sandan jihohi: Hadimin Buhari ya shawarci Tinubu ya rushe hukumomin tsaro 2, ya fadi dalilai

"Sai dai dole a hada kai idan har ana son cimma burin da ya saka aka kirkiri 'yan sandan."

Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sanda Gombe, ASP Mahid Mu'azu yaci tura saboda bai samu damar martani kan sakon da Legit Hausa ta aike masa ba.

Tinubu ya amince da ‘yan sandan jihohi

Kun ji cewa Shugaba Tinubu ya amince da kirkirar ‘yan sandan jihohi don dakile matsalar tsaron da ta addabi su.

Wannan na zuwa ne bayan ganawar da shugaban ya yi da gwamnonin jihohi kan matsalar tsaro da ya yi katutu a jihohinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.