Tsadar Rayuwa: Sarkin Kano Ya Tura Muhimmin Sako Ga Hukumar Kwastam, Ya Yi Gargadi

Tsadar Rayuwa: Sarkin Kano Ya Tura Muhimmin Sako Ga Hukumar Kwastam, Ya Yi Gargadi

  • Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya shawarci hukumar Kwastam kan irin yadda suke dakile kayan 'yan kasuwa
  • Sarkin ya bukaci hukumar da ta sakar wa 'yan kasuwar mara su gudanar da ayyukan kasuwancinsu ba tare da takura ba
  • Wannan na zuwa ne yayin da hukumar ke farautar wasu da ke fita da abincin yayin da ake cikin wani hali a kasa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ya bai wa Hukumar Kwastam shawara da ta bar ’yan kasuwa su gudanar da harkokin kasuwancinsu ba tare da tsangwama ba.

Sarkin ya ba da wannan shawara ne yayin da hukumar ke kama motoci makare da abinci kan zargin fitar da su waje.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta bankado hanyoyi 32 na safarar abinci daga Najeriya zuwa kasashen waje

Sarkin Kano ya shawarci Hukumar Kwastam kan kwace kayan 'yan kasuwa
Sarkin Kano bukaci Kwastam su sakarwa 'yan kasuwa mara su yi harkokinsu. Hoto: Sarki Ado Bayero.
Asali: Facebook

Wace shawara Ado Bayero ya bayar?

Ado Bayero ya ce ya kamata hukumar ta daga musu kafa su yi harkokinsu tare da musu katsalandan a kayansu ba matukar ba su karya dokar kasa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren yada labaran Masarautar, Abubakar Kofar Na’isa ya fitar.

Ya bayyana haka yayin karbar bakwancin Mataimakiyar Kwamandan Kwastam a yankin Kano da Katsina da Kaduna da Jigawa, Queen Ogbudu.

Ya bayyana yadda hukumar ke shiga kasuwanni tare da kwace kayan abinci a baya wanda a yanzu abin ya zama tarihi

Martanin hukumar Kwastam

Ya bukaci Hukumar da ta yi zama na musamman da ’yan kasuwar don kara wayar musu da kai kan irin kayan da ta ke so a shigo da su.

A bangarenta, Queen Ogbudu ta bayyana makasudin kawo ziyarar fadar Sarkin inda ta umarni ne daga shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta sake ba da sabon umarni ga likitoci kan 'yar Tiktok, Murja, ta fadi dalili

Ta ce ta kawo ziyarar ne don sanar da Sarkin umarnin Tinubu da su fitar da kayan abinci domin raba wa al’ummar kasa.

Wannan mataki ya biyo bayan ganin halin kunci da 'yan kasar ke ciki na tsadar rayuwa musamman kayan abinci.

Sarkin Musulmi ya yi gargadi

Kun ji cewa, Sarkin Musulmi, Sa'ad Abdubakar ya gargadi hukumomi kan halin da ake ciki.

Sultan ya ce a yanzu fa abin yafi karfinsu a matsayinsu na sarakunan gargajiya kan halin kuncin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.