Direbobin Dakon Mai Sun Dakatar da Yajin Aikin da Suke Yi a Fadin Kasar, an Gano Dalili

Direbobin Dakon Mai Sun Dakatar da Yajin Aikin da Suke Yi a Fadin Kasar, an Gano Dalili

  • Kungiyar masu motocin haya ta Najeriya (NARTO), ta sanar da dakatar da yajin aikin da ta shirya yi a fadin kasar.
  • Yusuf Lawal, shugaban kungiyar NARTO ya fitar da sanarwar janye yajin aikin a ranar Litinin a Abuja
  • Hakan ya biyo bayan ganawar da suka yi a ranar Litinin da gwamnatin tarayya da masu ruwa da tsaki bayan da direbobin sun dakatar da ayyukansu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Kungiyar masu motocin haya ta Najeriya (NARTO), ta dakatar da yajin aikin da ta shirya yi a fadin kasar.

Hakan ya biyo bayan ganawar da suka yi a ranar Litinin da gwamnatin tarayya da masu ruwa da tsaki bayan da direbobin dakon mai sun dakatar da ayyukansu.

Kara karanta wannan

Yajin aikin direbobin tanka: Matashi ya koka yayin da ya siya fetur kan N1,000 lita a jihar PDP

Direbobin NARTO sun janye yajin aiki, za su ci gaba da dakon fetur.
Direbobin NARTO sun janye yajin aiki, za su ci gaba da dakon fetur.
Asali: Facebook

Dalilin fara yajin aikin direbobin

Mambobin NARTO sun yi barazanar dakatar da aiki daga ranar Litinin saboda tsadar man dizal da suke amfani da shi a motocinsu na dakon man fetur.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yusuf Lawal, shugaban kungiyar NARTO ya sanar da janye yajin aikin a ranar Litinin a Abuja, Channels TV ta ruwaito.

Kamar man fetur wanda a yanzu ake sayar da shi akan naira 600 kan kowace lita, farashin dizal ya yi tashin gwauron zabi a yanzu.

Janye tallafin man fetur da tattalin arziki

A halin yanzu dai ana sayar da man dizal sama da naira 1,250 akan kowace lita a Najeriya.

Tun bayan da gwamnatin Tinubu ta janye tallafin man fetur, farashin sa ke ci gaba da haurawa sama ba tare da alamar sauka ba.

Janye tallafin man na daga cikin dalilan da suka jawo tabarbarewar tattalin arziki da kuma tsadar rayuwa a Najeriya kamar yadda masana suka bayyana.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Talakawa na murna yayin da farashin abinci ya fara sauka a Kano da wasu jihohin Arewa

Yajin aiki: Abun da gwamnati ta fadawa kungiyoyin kwadago

Legit ta ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta sasanta da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC bayan da suka yi barazanar tsunduma yajin aikin gargadi na kwanaki 14.

Kungiyoyin kwadagon sun ce za su shiga yajin aikin ne don nuna adawa kan tsadar rayuwa da ake fama da ita a kasar da kuma gazawar gwamnati na cika alkawurran da ta dauka.

A ranar Juma'ar da ta gabata, ministan kwadago da samar da ayyuka, Nkeiruka Onyejeocha ya ba kungiyoyin tabbacin cewa gwamnati za ta cika dukkan alkawurran da ta daukar masu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.