NYSC: Matasa Zasu Sha Jar Miya, Gwamnan PDP Zai Fara Ba Su Alawus N10,000 Duk Wata a Jihar Arewa
- Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya ɗauki alkawarin bai wa matasa ƴan bautar ƙasa alawus na N10,000 kowane wata
- Ya sanar da haka ne ranar Talata yayin da yake buɗe sansanin horar da matasan da ke Damare a karamar hukumar Girei, jihar Adamawa ranar Talata
- Ta bakin mataimakiyar gwamna, Fintiri ya ce duk wani ɗan bautar ƙasa ya zama cikakken ɗan jihar Adamawa kai tsaye
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Adamawa - Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayyana aniyar gwamnatinsa na bai wa matasa ƴan bautar ƙasa alawus duk wata a jihar Adamawa.
Gwamna Fintiri ya sanar da cewa gwamnatinsa zata riƙa biyan kowane kwafa da ke yi wa ƙasa hidima a jihar alawus ɗin Naira 10,000 kowane wata.
Fintiri ya bayyana haka ne yayin da yake ayyana buɗe sansanin horas da matasa ƴan hidima ga ƙasa na rukunin Batch 1 'A' 2024 waɗanda hukumar NYSC ta tura Adamawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda The Nation ta ruwaito, an kaddamar rukunin matasa ƴan bautar ƙasa a sasanin NYSC da ke Damare a karamar hukumar Girei, ranar Talata.
Meyasa gwamnan zai riƙa biyan alawus duk wata?
Gwamna Fintiri, wanda mataimakiyar gwamna, Farfesa Kaletapwa Farauta ta wakilta, ya ce wannan alawus ɗin zai taimaka wajen rage tasirin hauhawar farashi ga matasan.
A rahoton PM News, ya ce:
"Bana jin ko ɗar a zuciyata cewa zaku biya wannan karamcin da muka muku ta hanyar ƙwazo da himma a wuraren da za a tura ku domin ci gaban mutanen da suka karɓi bakuncin ku."
Fintiri ya jaddada cewa Adamawa gida ce ga dukkan matasa ƴan bautar ƙasa da suka baro gidajensu daban-daban domin yi wa kasarsu hidima.
Ya ci gaba da cewa:
"Daɗin daɗawa a matsayinku na masu yi wa kasa hidimi, kun zama cikakkun ƴan jihar Adamawa kai tsaye. Wannan gata ne da na baku a matsayina na lamba ɗaya kuma gwamnan jihar."
A nasa jawabin, shugaban NYSC na Adamawa, Jingi Denis, ya bayyana alawus na N10,000 a kowane wata a matsayin irinsa na farko a jihar tare da yabawa Fintiri bisa irin tallafin da yake bayarwa.
Faisal Musa, wani matashi da aka tura zuwa Adamawa domin hidima ga ƙasa ya tabbatar da wannan ci gaban ga wakilin Legit Hausa a wata hira ta wayar salula.
Matashin wanda ya kammala karatun digirinsa a jami'ar tarayya da ke Gashua a jihar Yobe, ya ce mataimakiyar gwamna ce ta rantsar da su a madadin mai girma gwamna.
Faisal, wanda ya karanci kwas ɗin kimiyyar siyasa, ya ce:
"A yau aka rantsar da mu watau aka buɗe sansanin horarwa a hukumance, mataimakiyar gwamna ce ta zo da kanta a madadin gwamna kuma ta yi jawabi mai ƙayatarwa.
"Eh tabbas ta ce za a riƙa biyan masu bautar ƙasa N10,000 duk wata, da yawa sun ji daɗin haka duk da kuɗin ba su taka kara sun karya ba amma wasu wuraren ba a ba da ko kwandala."
Jigon APC na neman jefa ministan Tinubu a rami
A wani rahoton kuma Jigon APC ya fallasa yadda ministan wutar lantarki ya yaƙi Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban ƙasa ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.
– Kehinde Olaosebikan ya ce gwamnatin shugaba Tinubu ba ta yi wa jam'iyyar APC ta jihar Oyo adalci ba duk da ƙuri'un da ta kawo a zaɓen da ya gabata.
Asali: Legit.ng