Tsadar Rayuwa: Kwastam Ta Fadi Abun Alkairi 1 da Za Ta Yi da Kayan Abincin da Ta Ƙwace

Tsadar Rayuwa: Kwastam Ta Fadi Abun Alkairi 1 da Za Ta Yi da Kayan Abincin da Ta Ƙwace

  • Hukumar kwastam ta Najeriya ta ce za ta fara raba kayan abincin da ta ƙwace daga hannun masu laifi don saukakawa 'yan kasar
  • Hukumar ta dauki wannan matakin ne tana mai la'akari da halin matsin tattalin arziki da tsadar abinci da ake fuskanta a fadin Najeriya
  • Hakazalika hukumar ta ce za ta tabbatar an yi adalci wajen rabon abincin bayan ta kammala gwada ingancinsu don gudun matsala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Hukumar hana fasa kwauri ta kasa (NCS), ta ce za ta rabawa 'yan Najeriya kayan abincin da ta ƙwace daga hannun masu laifi da nufin saukakawa mutane wahalar da ake ciki.

Hukumar ta ce za ta fara raba kayan ne da zaran an kammala yi masu gwaji don a tabbatar mutane za su iya amfani da su.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta bankado hanyoyi 32 na safarar abinci daga Najeriya zuwa kasashen waje

Tsadar rayuwa: Kwastam za ta raba kayan abincin da ta ƙwace.
Tsadar rayuwa: Kwastam za ta raba kayan abincin da ta ƙwace. Hoto: @CustomsNG
Asali: Twitter

A baya-bayan nan Legit Hausa ta ruwaito yadda 'yan Najeriya suka rinka gudanar da zanga-zanga a sassan kasar don nuna adawa da tsadar rayuwar da ake fuskanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manufar hukumar na rabawa mutane kayan abincin

Kwanturolan hukumar na kasa, Bashir Adewale Adeniyi a ranar Talata ya bayyana shirin da hukumar ta yi na raba kayan abincin, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce yana fatan hakan ya saukakawa mutane kan tsadar kayan abinci da ake fuskanta a kasuwannin kasar.

Mai magana da yawun hukumar, CSC Abdullahi Maiwada, a cikin wata sanarwa a shafin hukumar na X, ya ce shugaban hukumar ya dauki matakin don tabbatar da kokarin gwamnati na samar da abinci.

A cewarsa, hukumar ta dauki matakin don nuna muhimmanci yi wa al'umma hidima, wanda zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da dorewarsa.

Kara karanta wannan

Aiki na shine na biyu mafi wahala a duniya, Gwamnan CBN Cardoso

Hukumar za ta yi adalci wajen rabon abincin - Maiwada

Ya ce halin da ake ciki a kasar ya saka shugaban hukumar yanke hukuncin rabar da abincin domin cimma muradun Shugaba Bola Tinubu.

Maiwada ya yi nuni da cewa:

"Hukumar NCS za ta sanar da tsarin da za ta bi wajen rabon kayan abincin, kuma za ta tabbatar an yi adalci domin manufar shirin shi ne saukakawa 'yan Najeriya.
"Kafin fara rabon kayan, hukumar za ta fara tantance su don tabbatar da cewa mutane za su iya amfani da su gudun raba kayan da suka lalace da za su iya cutar da mutane."

Gwamnati ta gano hanyoyin da ake safarar abinci daga Najeriya

A safiyar Talatar nan ne Legit Hausa ta ruwaito cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce gwamnati ta bankado wasu hanyoyi 32 da ake safarar kayan abinci.

Hanyoyin wadanda ke a yankin Ilela, Shettima ya ce ana fitar da kayan abinci daga Najeriya a kai su ƙasashen makwabta.

A cewarsa, irin wannan ne ke jawo hauhawar farashin kayan abincin, inda ya yi nuni da cewa an kama motoci 45 dauke da masara za a kai Nijar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel