Mun Gaji Tsadar Rayuwa Ce Daga Buhari, Ministan Tinubu Ya Fadi Tsarin da Suke Bi Don Dakile Hakan

Mun Gaji Tsadar Rayuwa Ce Daga Buhari, Ministan Tinubu Ya Fadi Tsarin da Suke Bi Don Dakile Hakan

  • Yayin da ake cikin wani hali a Najeriya, Ministan Tinubu ya fadi hanyoyin da suke bi don dakile matsalar tsadar rayuwa
  • Ministan Kudi a Najeriya, Wale Edun ya ce dukkan wannan wahalar sun gaje ta a mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari
  • Wale ya ce gwamatin Tinubu ta na kokarin samar da hanyoyin rage farashin kaya da tsadar rayuwa a Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ministan Kudi a Najeriya, Wale Edun ya bayyana irin matakan da suke dauka don rage farashin kaya a kasar.

Ministan ya ce gwamnatin Tinubu ta gaji tsadar rayuwar ce daga tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Atiku ya fadi yadda Tinubu ya haddasa tashin Dala da rugujewar tattali a wata 8

Ministan Tinubu ya ce sun gaji tsadar rayuwa ce daga Buhari
Wale Edun ya bayyana hanyoyin da suke bi don dakile matsalar tsadar abinci. Hoto: Bola Tinubu, Wale Edun.
Asali: Twitter

Mene Ministan Tinubu ke cewa kan tsare-tsarensu?

Wale ya ce gwamatin Tinubu ta na kokarin samar da hanyoyin rage farashin kaya da tsadar rayuwa a Najeriya baki daya, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Edun ya bayyana haka ne a yau Talata 20 ga watan Faburairu a birnin Tarayya Abuja yayin wani babban taro.

Ministan ya tabbatar da wahalar da ake sha a kasar inda ya bayyana hanyoyi da kuma kokarin dakile matsalar a kasar.

Wane kokari gwamnatin Tinubu ta ke yi?

Ya ce a kokarin gwamnatin don ganin an dakile matsakar, Tinubu ya ba da umarnin fitar da tan dubu 42 na hatsi don magance matsalar.

Har ila yau, ya ce nan gaba kadan za a sake fitar da tan dubu 60 ga 'yan kasar don rage musu halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnonin PDP sun nemi Tinubu ya yi murabus, sun fadi dalili

Wannan na zuwa ne yayin da ake cikin matsanancin halin matsin rayuwa da tsadar kayayyakin a kasar, cewar Premium Times.

Wannan wahala ba ta rasa nasaba da tsare-tsaren tattalin arziki da Shugaba Tinubu ya yi musamman cire tallafin mai.

Majalisar ta yi alkawari ga 'yan Najeriya

Kun ji cewa Majalisar Dattawa ta yi alkawarin hana duk wani shiri na kara kudin mai da wutar lantarki.

Majalisar ta ce su na kokarin yin hakan ne don kishin 'yan Najeriya wanda don su suke majalisar ba don kansu ba.

Wannan na zuwa ne yayin da ake jita-jitar cewa za a cire tallafin wutar lantarki bayan cire na man fetur a watan Mayun 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.