Babban Labari: EFCC Ta Cafke ’Yan Canji a Abuja, an Gano Dalili

Babban Labari: EFCC Ta Cafke ’Yan Canji a Abuja, an Gano Dalili

  • Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta kai sumame ofishin wasu 'yan canjin kudi a Abuja, sun yi awon gaba da mutane
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake canja dalar Amurka 1 akan N1,725 a kasuwar canji da ke babban birnin tarayyar kasar
  • Akalla 'yan canji 50 ne aka ruwaito hukumar EFCC ta cafke a Wuse Zone 4, wanda ake hasashen zai dakile tsadar canjin kudin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Darajar Naira na ci gaba da faduwa a kasuwar canji da ta hada-hadar kudade, kamar yadda rahotannin kasuwar ya nuna a ranar Litinin

A halin da ake ciki, darajar Naira ta fadi zuwa N1,730 akan kowacce dala 1, yayin da a wasu wuraren kuma ake cikinta kasa da hakan.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Bayan Kano da Minna, sabuwar zanga-zanga ta barke a wata jihar Kudu

EFCC ta kama ’yan canji a Abuja
EFCC ta kama ’yan canji a Abuja da ake zargin suna tsawwala farashin dala akan Naira. Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

Biyo bayan tsadar canjin kudin, rahotan The Punch ya nuna cewa jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) sun kai sumame ofisoshin 'yan canji na Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Darajar Naira na ci gaba da faduwa a kasuwar bayan fage

A yayin sumamen, an ruwaito cewa sun kama mutane da dama wadanda ake zargin su ne ke tsawwala farashin canjin Naira akan dala.

Naira dai ta samu faduwar kaso 3.59% daga N1,670 da aka yi cinikin ta akan kowacce dala a ranar Juma'a a kasuwar bayan fage.

Faduwar darajar Naira ya kara ta'azzara ne sakamakon neman dala da ya karu a Abuja da kuma boye kudin da wasu suka yi.

Wannan na zuwa duk da babban bankin kasar (CBN) ya dauki matakin bunkasa samar da dalolin a kasuwar hada-hadar kudi ta duniya.

Kara karanta wannan

Jerin jihohin Najeriya 10 da aka fi samun kayan abinci da tsada, Kogi na kan gaba

Dalilin hauhawar farashin Dala akan Naira

An ruwaito cewa 'yan canji a Legas da Abuja na sayar da $1 akan N1,700 yayin da su suke sayen dala daya akan N1,730.

Wani ɗan canji a kasuwar bayan fage ta Wuse, Abuja, Mista Abubakar Taura ya ce:

"Kwastomomi na neman dala yanzu ruwa a jallo, wanda ya jawo ta yi tsada a kasuwar.,"

Wani dan canji, Ibrahim Yahu ya ce suna sayar da $1 akan N1,725 a filin jirage na Abuja saboda yadda matafiya ke neman dalar ruwa a jallo.

A hannu daya kuma,.ana hada-hadar Euro 1 akan N2,000 a kasuwar canji a ranar Litinin amma ana sayar da ita akan N1,931 a farashin gwamnati, a cewar CBN.

Jami'an EFCC sun kama 'yan kasuwar canji mutum 50

Wannan ya zaburar da jami'an hukumar EFCC suka dira kasuwar 'yan canji ta Wuse Zone 4, Abuja, inda suka yi awon gaba da akalla 'yan canji 50.

Kara karanta wannan

Tsadar abinci: Gwamnati ta rufe wani babban kanti a Abuja, an samu cikakken bayani

A cewar wani dan canji, Abubakar Taura wanda abin ya faru akan idonsa, ya ce jami'an sun kai sumamen ne a ranar Litinin.

Ya ce:

"A ranar Litinin misalin karfe 3 na rana, jami'an hukumar EFCC suka kawo mana sumame, suka tafi da mambobinmu kusan mutum 50.
"Sun yi ikirarin cewa 'yan canji ne suka jawo darajar Naira ke ci gaba da faduwa a kasuwar bayan fage da ma ta hada-hadar kudi."

Sai dai har zuwa wallafa wannan labarin, ba a samu samar tantance labarin daga hukumar EFCC ba.

Darajar Naira ta sake faduwa ƙasa, $1 ta haura N1,600

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa Naira ta sake faduwa a kasuwar hada-hadar kudi ta duniya yayin da darajar dala ta haura N1,600.

A ranar Alhamis da ta gabata, an canja $1 akan N1,600 sabanin N1,503.38 da aka yi cinikinta akan kowacce dala a ranar Laraba.

Masu fashin baki kan harkokin tattalin arziki sun nuna damuwar su kan matakan tattali da gwamnatin Tinubu ke dauka wanda ya jefa kasar a tsadar rayuwa a tabarbarewar tattalin arzikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.