Ku Bamu Kwana 30, Masu Sarrafa Siminti Sun Gindaya Sharuda Ga Tinubu Kan Farashin, Sun Kawo Mafita
- Masu sarrafa siminti sun bai wa Gwamnatin Tarayya sharadi don daidaita farashin siminti a kasar
- Shugaban kungiyar, David Iweta ya bayyana babban dalilin tashin farashin da cewa neman simintin yafi yawansa
- Ya bukaci Tinubu ya duba dokar da tsohon shugaban kasa, Marigayi Umaru Musa Yar'adua ya yi kan harkar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Kungiyar masu sarrafa siminti a Najeriya (CEPAN) ta ce a shirye take don karyar da farashin simintin a cikin wata daya.
Shugaban kungiyar, David Iweta shi bayyana haka inda ya ce idan har gwamnati za ta tafi tare da su hakan mai sauki ne.
Mecece mafita kan tsadar siminti?
Iweta ya kwatanta tsadar kayan da yawan neman simintin da ake yi wanda ya fi karfin abin da ake samarwa a kasar, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
David ya ce tuntuni kungiyarsu ta hango irin wannan matsalar inda ta gargadi gwamnati kan illar hakan wurin bai wa ‘yan siraru lasisi.
A cewarsa:
“Abin da yanzu muke fuskanta shi ne neman simintin da ake yi yafi karfin abin da muke samarwa a kasar, mu a kungiya mun san haka zai faru.
“Kuma ya faru ne saboda wasu ‘yan tsiraru ne kawai ke da damar samar da simintin wanda ba za su iya wadatar da kasar ba.”
Wane gargadi suka yi a baya?
Ya ce kungiyar ta yi gargadi tun ana siyar da simintin dubu uku inda ta ce idan ba a dauki matakai ba zai iya kai wa dubu tara.
Iweta ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta yi duba zuwa matakan da marigayi tsohon shugaban kasa, Musa Yar’adua ya yi a wancan lokaci.
Yar’adua ya bai wa wasu lasisin shigo da simintin amma aka samu matsala wasu marasa kishin kasa suka hana ruwa gudu.
Ya ce an kawo tsarin ne don dakile ratar da ke tsakanin yawan samar da simintin da kuma bukatar shi a kasar, cewar Nairametrics.
Ya ce:
“Hanya mafi sauki ga gwamnati ita ce sake duba tsari irin na Yar’adua, idan ba haka ba farashin zai yi ta tashi saboda wadannan ba za su iya wadatar da kasar ba.”
Gwamnati za ta zauna da Dangote da BUA
Kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta bukaci zama da Aliko Dangote da kuma Abdussamad Rabiu BUA kan tsadar siminti.
Wannan ganawa na zuwa ne yayin da ake fama da tsadar simintin wanda ya kai har naira dubu takwas.
Asali: Legit.ng