Labari Mai Dadi: FG Ta Fara Biyan Albashin Malaman Jami'a Na ASUU da Aka Rike Bayanai Sun Fito
- Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya fara biyan albashin malaman jami'o'i na ƙungiyar ASUU da aka riƙe
- Gwamnatin tarayyar ta fara sakin albashin ne na wata huɗu cikin na wata takwas da aka riƙe sakamakon amincewa da hakan a watan Oktoban 2023
- Albashin na wata takwas dai an riƙe shi ne a lokacin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, bayan ASUU ta shiga yajin aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta fara biyan albashin malaman jami’o’i a ƙarƙashin ƙungiyar malaman jami’o’i ta ASUU da aka riƙe.
Majiyoyi da dama a ɓangaren ilimi sun tabbatar wa jaridar The Punch fara biyan albashin a ranar Litinin.
Shugaban ASUU na jami’ar fasaha ta tarayya da ke Minna, Farfesa Gbolahan Bolarin, ya tabbatar da faruwar lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamansa:
"Eh gaskiya ne. An fara biyan kuɗin."
Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya shaida wa jaridar TheCable cewa ya samu rahoton cewa wasu daga cikin mambobin ƙungiyar, an biya su na wata ɗaya ko wata biyu.
A watan Oktoban 2023 ne shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da sakin albashin wata huɗu daga cikin na wata takwas da aka riƙe na malaman jami'o'in.
An hana biyan albashin ne a lokacin da gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta sanya dokar ‘ba aiki, ba biya’ akan wasu ƙungiyoyin jami’o’i da suka fara yajin aikin da ya kwashe watanni takwas ana yi a shekarar 2022.
Ministan Tinubu ya cire malaman jami'a daga IPPIS
Kwanan nan ministan Ilimi Tahir Mamman ya sanar da yin ƙarin albashin ma’aikatan jami’a da kaso 35%.
Ya kuma bayyana cewa jami’o’i sun samu ƴancin cin gashin kansu tare da cire su daga tsarin IPPIS.
Mamman ya ƙara da cewa a yanzu jami'o'i za su iya ɗaukar ma'aikata tare da cike guraben aiki ba tare da neman izni ba.
ASUU Ta Fara Shirin Yajin Aiki
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar malaman jami'o'i ta ASUU ta nuna damuwarta kan yadda gwamnati ta ƙi cika yarjejeniyar da suka ƙulla.
Ƙungiyar ta yi nuni da cewa rashin cika wannan yarjejeniyar ka iya kai ta ga tsunduma yajin aiki domin ganin an cika alƙawari.
Asali: Legit.ng