Farfesa Ya Bayyana Kuskuren da Tinubu Ya Fara Tafkawa Tun Kafin Ya Shiga Aso Villa
- Farfesa Kabiru Isa Dandado ya soki yadda Bola Tinubu ya sanar da janye tsarin biyan tallafin fetur ranar da aka rantsar da shi
- Tsohon kwamishinan kudin na jihar Kano yake cewa matakin da sabon shugaban kasa ya dauka ne ya tashi farashin kaya a kasar
- Dandado ya hango matsaloli idan gwamnatin Bola Tinubu ba ta magance hauhawan farashi musamman na kayan abinci ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kano - An shiga wani mummunan yanayi na tattalin arziki a Najeriya musamman tun daga tsakiyar shekarar 2023 zuwa yanzu.
Ganin yadda abubuwa su ka cabe, tashar BBC Hausa ta zanta da Farfesa Kabiru Isa Dandado a ranar Lahadi domin jin matsayarsa.
Masanin tattalin arzikin ya nuna halin da aka shiga na tsadar rayuwa da tashin farashin kaya yana neman wuce tunani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu yana cikin barazanar tattali
Farfesa Kabiru Dandado ya bayyana cewa gwamnati tana fuskantar barazana saboda yadda ta gaza hana farashin kaya tashi.
"Wannan yana nuna akwai hadari babba a kokarin da ake gani gwamnati za ta iya wajen dakile talauci"
"Domin mafi yawan ‘yan kasa ba za su iya jure wannan hauhawar farashin ba."
"Za a iya dibar mutane a shigar da su cikin satar mutane a karbi kudin fansa, fashi da makami sa sauransu."
- Farfesa Kabiru Isa Dandado
Farfesan Akantancin na jami’ar Bayero da ke Kano ya shaidawa tashar rediyon cewa tun farko Bola Ahmed Tinubu ya yi kuskure.
Daga rantsar da shi a watan Mayun bara, shugaban kasar ya sanar da cire tallafin fetur, Farfesan yana zargin an yi saurin sanarwa.
Wannan gwamnati ta Bola Tinubu tayi mummunan kuskure, maganar cire tallafin fetur bai kamata ya shiga bayanin shugaban kasa ba na kaddamarwa
Wannan lokaci ne na yin bayanai na farantawa kasa, na sa wa ‘yan kasa karfin gwiwa. Cire wannan ya jefawa ‘yan kasa bam na fuskantar tsadar kayayyaki.
- Farfesa Kabiru Isa Dandado
Tsohon kwamishinan kudin ya ce sauran matakan da ake dauka na rufe shaguna da tunanin shigo da abinci za su kashe zukatan mutane.
Tinubu ba zai bude iyakoki ba
Rahoto ya zo mana cewa Bola Ahmed Tinubu ya ki daukar shawarar Kashim Shettima a kan kayyade farashin abinci a Najeriya.
Sannan gwamnatin tarayya ta yi jan-kunne kan hadarin bude iyakoki domin a shigo da abinci, Tinubu yana ganin hakan ba mafita ba ce.
Asali: Legit.ng