Bidiyon Fasto Na Kokarin Warkar da Wani Mahauci Ya Ja Hankalin Mutane, An Kwashi 'Yan Kallo

Bidiyon Fasto Na Kokarin Warkar da Wani Mahauci Ya Ja Hankalin Mutane, An Kwashi 'Yan Kallo

  • Jama'a sun yi cece-kuce kan wani bidiyo da ya yadu inda aka nuno wani fasto yana yi wa mahaukaci addu'a babu kakkautawa
  • Mutane sun taru a wajen mahaukacin da fasto yayin da suka zura ido suna kallon yadda za ta kaya a tsakaninsu
  • Wasu mutane sun sha dariya kan yadda aka kwashi 'yan kallo tsakanin mahaukacin da malamin addinin, da sauran mutane

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Bidiyon wani fasto da wani mahaukaci suna fafatawa da junansu kan titi ya haddasa cece-kuce a tsakanin jama'a a soshiyal midiya.

Mutumin da ke da lalurar tabin hankalin ya kasance gajere kuma kafarsa babu takalmi yayin da ya dunga nuna turjiya ga abin da faston ke yi.

Fasto ya yi kokarin warkar da mahaukaci
Bidiyon Fasto Na Kokarin Warkar da Wani Mahauci Ya Ja Hankalin Mutane, An Kwashi 'Yan Kallo Hoto: @hk.dollars5
Asali: TikTok

A bidiyon TikTok wanda @hk.dollars5 ya yada, an gano inda faston sanye da farin kaya ya daura hannunsa a kan mahaukacin yayin da yake yi masa addu'a.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun kashe masallata 3 tare da sace wasu da dama a jihar Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane sun taru a kansu, suna ta daukar bidiyon lamarin da wayoyinsu. Har zuwa karshen bidiyon, mahaukacin bai dawo cikin hayyacinsa ba.

Ra'ayoyin jama'a sun sha bamban akan bidiyon.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun sha dariya kan bidiyon

user9572458962580 ya ce:

"Me ya faru ne wai, sai danna mani kai kake kai kake son kashe ni ne wai??? Gwanda ka bar ni da hauka na faaa, ko dai so kake na dawo daidai na fara biyan kudaden abubuwa."

Ademola ya ce:

"Gayan fadi yake ÿi abin da za ka yi abin da zan yi yana zuciyata kuma sai na aikata."

Okay_FK ya ce:

"Ta yaya faston nan ya iya barin wannan wuri bayan adduársa da bata ci ba."

Official presh ya ce:

"Yallabai ka kyale mutumin nan baya so ya fadi."

Kara karanta wannan

Kasar Girka ta kuduri aniyar halatta auren jinsi, da daukar rainon yara

emmystarr3 ya ce:

"Fasto zai yi danasanin abin da yasa ya fara wannan addu'ar."

Lauyoyi sun yi doke-doke a cikin kotu

A wani labari na daban, a cikin wani faifan bidiyo da aka yada, an gano wasu lauyoyi na fada a cikin kotun majistare da ke jihar Enugu.

Jaridar Punch ta tattaro cewa hatsaniyar ta afku ne a yau Juma’a 13 ga watan Oktoba yayin zama a kotun majistare a Nsukka da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng