Kano: An Yi Korafi Yayin da Abba Kabir Ya Ware N5.32bn Don Abinci da Gyararraki a Gidan Gwamnati

Kano: An Yi Korafi Yayin da Abba Kabir Ya Ware N5.32bn Don Abinci da Gyararraki a Gidan Gwamnati

  • Yayin da ake cikin matsin tattalin arziki, Gwamna Abba Kabir ya ware wasu kudade don abinci da gyara a gidan gwamnati
  • Masu saka ido sun koka kan yadda aka ware kudaden don gyaran gidan gwamnati da kuma gidan gwamnan a Kwankwasiyya City
  • Hadimin gwamnan, Sanusi Bature ya tabbatar da cewa gwamnatin ta kasha miliyoyin kudade kan gyararrakin sai dai bai bayyana adadin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – An yi ta cece-kuce bayan Gwamna Abba Kabir ya ware biliyan biyar da doriya kan abinci da gyararraki a gidan gwamnati.

Kudaden na cikin kasafin kudin shekarar 2024 ne da gwamnan ya sanya wa hannu a shekarar da ta gabata, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya ki karbar shawarar bude iyakoki da kayyade farashin abinci

Yawan biliyoyin kudade da Abba Kabir ya ware a kasafin wannan shekara
Wasu sun nuna damuwa kan kudaden da Abba Kabir ya ware a kasafin bana don wasu ayyuka. Hoto: Abba Kabir.
Asali: Twitter

Ya kasafin kudin ya kasance?

A cikin kasafin gwamnan ya ware miliyan 800 don gyaran ofishinsa a gidan gwamnati da kuma miliyan 500 na gidansa a Kwankwasiya City da ke birnin Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya kuma ware miliyan 200 don gina sabon loginsa a Kwankwasiyya City kamar yadda Premiuim Times ta binciko.

Hadimin gwamnan, Sanusi Bature ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta kasha miliyoyin kudade kan gyararrakin sai dai bai bayyana adadin ba.

Abba Kabir ya kuma ware miliyan 15 don gina dakin taro a gidan gwamnati da miliyan 20 don gina dakunan kwana biyu a gidan gwamnatin.

Wasu sun yi korafi kan lamarin

Har ila yau, an ware dubu 775,860 don abinci da kayan shaye-shaye sannan miliyan 800 na tsaro da kuma miliyan 800 na wasu ayyuaka daban.

A cikin kasafin har ila yau, an ware miliyan 232 na tafiye-tafiye sannan miliyam uku na tangaraho da wasu miliyan uku na ‘Data’ sai kuma miliyan 4.6 na tashoshin talabijin.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya ba jami'an tsaro umarnin cafke masu boye kayan abinci

Gwamnan ya kuma ware miliyan 90 na man fetur da bakin mai sai miliyan 38 na motoci da miliyan 47 na man fetur a janareta.

Wasu masu saka ido kan lamarin sun koka kan yadda za a kashe wadannan kudaden musamman ganin halin matsin tattalin arziki da ‘yan jihar ke ciki.

Sun bukaci yin amfani da wadannan kudaden da aka samu bayan cire tallafi don taimakawa marasa karfi da gajiyayyu.

Sun koka kan yadda yara wadanda basa zuwa makaranta suka cika birnin Kano da kuma matsalolin kiwon lafiya a jihar.

Ganduje ya rasa jiga-jigan APC

Kun ji cewa shugaban jam’iyyar APC, Umar Ganduje ya tafka asara bayan wasu sun koma NNPP.

Akalla ciyamomin kananan hukumomi uku ne suka sauya sheka zuwa NNPP bayan watsar da APC a Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel