Gwamnan Arewa Ya Bukaci Ayi Abu 1 Don Kawo Karshen Matsalar Tsaro
- Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya yi ta'aziyya kan sabbin hare-haren da ƴan bindiga suka kai a wasu sassan jihar
- Gwamnan ya buƙaci jami'an sojoji da su ƙara ƙaimi wajen ganin sun fatattaki ƴan ta'adda a faɗin jihar
- Malam Uba Sani ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba d amayar da hankali kan ƙoƙarinta na ganin ta shawo kan matsalar rashin tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jiihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya roƙi sojoji da su ƙara ƙaimi wajen fatattakar ƴan bindiga a faɗin jihar.
Hakan ya biyo bayan hare-haren da aka kai a ƙananan hukumomin Igabi da Kauru, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wasu mutane tare da yin garkuwa da wasu, cewar rahoton Daily Trust.
Gwamna Uba Sani ya samu wakilcin kwamishinan ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, a ƙauyukan Gwada da Kerawa da ke ƙaramar hukumar Igabi a yayin tantance halin da ake ciki a yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya kuma miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa ransu a Igabi da Kauru, rahoton TheCable ya tabbatar.
Kwamishinan ya kasance tare da Kwamandan runduna ta ɗaya ta Najeriya, Birgediya Janar Muhammad Kana, tare da sauran kwamandojin soji da jami’an tsaro da ke aiki a yankunan.
Wane ƙoƙari gwamatin take yi?
A kalamansa:
"Muna nan a madadin Gwamna Uba Sani domin mu yi ta’aziyyar rayukan da aka rasa a ƙauyukan Kerawa da Sabon Birni a ƙaramar hukumar Igabi da kuma ƙauyukan Kwassam, Kurera, da Kan Makama a ƙaramar hukumar Kauru.”
"Ina so in tabbatar muku da cewa mun zo ne domin duba yanayin tsaro, kuma kamar yadda kuke gani, a yanzu haka sojoji suna gudanar da ayyuka a waɗannan wurre, wanda kun shaida.
"Gwamnatin jiha ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba a ƙoƙarinta, sannan tana kuma aiki don ganin an ci gaba da kai hare-haren sojoji a wuraren da ake da matsalar ƴan ta'adda kamar ƙaramar hukumar Kauru."
DPO Ya Samu Kyauta a Kaduna
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙaramar hukumar Kagarko da ke jihar Kaduna, Hon. Nasara Rabo, ya ba wa wani jami’in ‘yan sanda (DPO) mai suna Idris Ibrahim kyautar naira miliyan 1.
Honorabul Rabo ya ba wa DPO tukuicin ne saboda ya ƙi amincewa da karɓar makudan kudade da wani mai garkuwa da mutane ne ya bayar domin a datse bincikensa.
Asali: Legit.ng