‘Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Jihar Arewa, Sun Tafka Barna
- Wasu tsagerun 'yan bindiga sun kai kazamin hari kauyukan Dekko, Lama da Monkin a karamar hukumar Zing ta jihar Taraba
- 'Yan bindigar da ake tunanin masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da mutane 16 a yayin harin da suka kai a daren ranar Jumaá
- Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, amma ta ce tana jiran karin bayani kan adadin mutanen da aka sace
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Jihar Taraba - Wasu 'yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun farmaki kauyuka uku a karamar hukumar Zing ta jihar Taraba.
Yayin harin da aka kai a daren Juma'a, 16 ga watan Fabrairu, maharan sun yi garkuwa da mutane 16 ciki harda wani malamin addini.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan bindigar da yawansu sun farmaki kauyukan Dekko, Lama da Monkin a daren Juma'a sannan suka yi awon gaba da mutanen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tattaro cewa mutanen kauyukan da dama sun jikkata sakamakon harbin bindiga yayin da suke kokarin tserewa saman tsaunuka yayin hare-haren.
An rahoto cewa 'yan bindigar wadanda suka zo kan babura sun kai su fiye da 100.
Wata majiya daga yankin ta ce 'yan bindigar na cikin 'yan ta'addan da rundunar soji da maharba suka fatattaka kwanan nan daga yankunan tsauni a karamar hukumar Yorro ta jihar.
Rundunar 'yan sanda ta yi martani
Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Taraba, SP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai kuma ya ce yana jiran karin bayani da ainahin adadin mutanen da aka sace daga DPO na yankin Zing.
'Yan bindiga sun farmaki garuruwan Kaduna
A wani labarin, Legit Hausa ta rahoto cewa 'yan bindiga sun kashe mutum tara a garin Kwasam, karamar hukumar Kauru da garin Gwada a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa maharan sun kuma yi garkuwa da mutum 35, ciki harda wani daraktan Babban Bankin Najeriya (CBN) mai ritaya, kaninsa da matar kaninsa.
A cewar majiyoyi, 'yan bindigar sun kuma jikkata mutum tara a hare-haren da suka kai kananan hukumomin biyu.
Asali: Legit.ng