Gwamnatin Tarayya Za Ta Yi Ganawa Ta Musamman da Dangote, BUA Kan Wani Dalili, Bayanai Sun Fito

Gwamnatin Tarayya Za Ta Yi Ganawa Ta Musamman da Dangote, BUA Kan Wani Dalili, Bayanai Sun Fito

  • Yayin da ake fama da tsadar kaya musamman bangaren siminti, Gwamnatin Tarayya ta kira ganawa ta musamman
  • Ministan Ayyuka, Dave Umahi shi ne ya bukaci ganawar da masu sarrafa siminti a kasar kamar Dangote da BUA da kuma Lafarge
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wani mai siyar da siminti kan wannan mataki da Gwamnatin Tarayya ta dauka yayin da siminitn ya yi tsada

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayya za ta yi zama da Alhaji Aliko Dangote da Abdussamad Rabiu da kamfanin Lafarge kan tsadar siminti.

Ministan Ayyuka, Dave Umahi shi ya kira ganawar yayin da farashin siminti ya kara tsada a ‘yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnonin PDP sun nemi Tinubu ya yi murabus, sun fadi dalili

Gwamnati ta bukaci zama na musamman da Dangote da BUA
Gwamnati za ta yi zama da Dangote da BUA da kuma Lafarge kan tsadar siminti. Hoto: Aliko Dangote, Abdussamad Rabiu.
Asali: Getty Images

Mene dalilin zaman da Dangote da BUA?

Farashin simintin ya tashi daga dubu hudu a makwanni kadan zuwa dubu takwas har dubu 10, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangote da BUA da Lafarge na daga cikin masu samar da simintin a kasar wanda Ministan ya bukaci zama da su.

Hadimin Ministan, Orji Uchenna Orji shi ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a jiya Juma’a 16 ga watan Faburairu.

Sanarwar ta ce:

“Yayin da farashin simintin ke kara tsada duk da bukatar simintin daga 'yan Najeriya, Minista Dave Umahi ya bukaci ganawar gaggawa da masu kamfanonin simintin.”

Orji ya ce Ministan ya koka kan yadda aka samu rata sosai a farashin simintin a kamfanonin da kuma kasuwanni, NairaMetrics ta tattaro.

Bukatar Umahi kan tsadar simintin a Najeriya

Ya kara da cewa:

“Wannan a bayyane ya ke masu kamfanonin su na fama da matsalolinsu wanda dole za mu duba hakan.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya tona yadda Gwamnatin Buhari ta ‘saida’ man shekaru masu zuwa

“Amma a binciken da muka yi akwai rata sosai a farashin da ake samu daga kamfanin da kuma wurin ‘yan kasuwa.
“Dole mu duba lamarin da sauran matsaloli ko kalubale don neman hanyar kawo sauki.”

Legit Hausa ta ji ta bakin wani mai siyar da siminti kan matakin Gwamnatin Tarayya:

Alhaji Sani mai bulok ya ce gaskiya ba sa jin dadin yadda simintin ke kara tsada saboda su ma ya na shafarsu.

Ya ce:

"Wasu su na tunanin wai tsadar abu alkairi ne a gare su idan su na siyar da shi, amma ni abin da na fahimta shi ne tsadar kaya ya na rage ciniki.
"Musamman mu da muke siyar da kayan a yankin marasa karfi da abinci za su ji ko kuma siyan siminti, ya ce ya kamata a yi wani abu kai gaskiya."

Tinubu ya amince da ‘yan sandan jihohi

Kun ji cewa Shugaba Tinubu da gwamnaonin Najeriya sun amince da kirkirar ‘yan sanda jihohi don dakile matsalolin tsaro musamman a jihohi.

Wannan na zuwa ne bayan wata ganawa da shugaban ya yi da gwamnonin don neman mafita a rashin tsaro da tsadar rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel