Babban Nasara: Dakarun Sojoji Sun Samu Gagarumar Nasara Kan 'Yan Ta'aɗda, Sun Halaka da Dama
- Hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta sanar da nasarar da dakarun sojoji suka samu a cikin mako ɗaya a faɗin ƙasar nan
- Daraktan yaɗa labarai na DHQ ya bayyana cewa sojojin sun halaka ƴan ta'adda 254 tare da cafke wasu 264 a faɗin ƙasar nan
- A yayin samamen daban-daban, dakarun sojojin sun kuma ƙwato mugggan makamai masu yawa daga hannun ƴan ta'addan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Sojojin Najeriya sun kashe ƴan ta'adda 254 tare da kame wasu 264 a cikin mako guda yayin samamen da sojojin suka kai a faɗin ƙasar nan.
Daraktan yaɗa labarai na hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ), Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Juma’a, 16 ga watan Fabrairun 2024, cewar rahoton Channels tv.
A kalamansa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A cikin makon da ake bita sojoji sun samu nasarori kamar haka: Sojojin sun kashe ƴan ta'adda 254 tare da kama 264 daga cikinsu.
"A ci gaba da gudanar da ayyukan yaƙi da ta’addanci da na ƴan tada ƙayar baya, sojojon sun hana waɗannan miyagun cimma manufofinsu.
Buba ya kuma nanata ƙudurin rundunar na rage ƙarfin ƴan ta’adda na kai ƙananan hare-hare da nufin haifar da firgici a yankunan da ake gudanar da ayyukan samar da tsaro a faɗin ƙasar nan, rahoton PM News ya tabbatar.
Sojoji sun hana ƴan ta'adda sakat
Kakakin na DHQ ya bayyana cewa dakarun sojojin sun gudanar da yaki a kan masu yi wa tattalin arzikin ƙasar zagon kasa, yana mai jaddada cewa an kama barayin man fetur guda 104 yayin da aka ceto mutum 73 da aka yi garkuwa da su.
A cewar Buba, sojoji sun hana ɓarayin man fetur ɗin samun kuɗaɗen da aka ƙiyasta kimanin Naira biliyan 2.6 a shiyyar Kudu-maso-Kudu.
Abubuwan da aka ƙwato daga hannun wadanda ake zargin sun haɗa da makamai iri-iri guda 378 da alburusai iri-iri guda 4,705.
Legit Hausa ta sami jin ta bakin wani Malam Muhammad Lawal wanda ya nuna jindaɗinsa kan wannan gagarumar nasarar da dakarun sojojin suka samu.
Ya bayyana cewa sojojin sum zama abun alfahari saboda yadda suke sadaukar da kansu da jajircewa domin ganin sun ragargagji ƴan ta'adda.
Ya kuma yi addu'ar Allah ya ci gaba da ba su nasara a ƙoƙarin da suke yi na ganin sun kawo ƙarshen miyagu a faɗin ƙasar nan.
DHQ Ta Faɗi Hanyar Magance Rashin Tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana hanyar da za a kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a Najeriya.
DHQ ta bayyana cewa idan ana son ganin an kawo ƙarshen matsalar, dole ne ƴan Najeriya su kasance masu kishin ƙasarsu.
Asali: Legit.ng