Wata Mata Ta Sume Saboda Matsin Rayuwa, Bata Iya Ciyar da Yara 4 da Mijinta Ya Mutu Ya Bari
- Wata mata da mijinta ya mutu ta fadi sumammiya a titi yayin da take hanyarta na zuwa rokon ruwan leda daga wajen bayin Allah
- A cikin wani bidiyo, an hasko matar zaune a kasa yayin da mutanen da ke wajen suke kokarin dawo da ita kan kafafunta
- An tattaro cewa matalauciyar matar ta gaza ciyar da yaranta tsawon kwanaki biyu duk da cewar tana aiki tukuru
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
'Yan Najeriya sun nuna aniyarsu ta son taimakawa wata mata da mijinta ya mutu wacce ta sume a kan hanya saboda wahalar rayuwa.
Wani bidiyo da ya yadu ya nuno matar zaune a kasa yayin da mutane suka taru a kanta suna ta kokarin dawo da ita kan kafafunta.
Matar da mijinta ya rasu ta gaza ciyar da yara 4
Matar wacce ke da yara hudu ta shiga wani hali saboda tsadar rayuwa da ake ciki a kasar kuma saboda haka, bata iya daukar dawainiyar yaranta su hudu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tattaro cewa matar ta je rokon ruwan piya wata ne bayan ta gaza ciyar da yaranta tsawon kwanaki hudu.
Cikin haka ne ta sume sannan mutanen da suka ga lokacin da ta yanke jiki ta fadi suka gaggauta ceto ta.
Jama'a sun yi martani yayin da wata mata ta sume
Masu amfani da soshiyal midiya sun koka sosai kan halin da ake ciki na tsadar rayuwa a kasar.
Strictlymeee ta ce:
"Bari na taimaka mata don Allah. Wani ya nemota ."
Macdenemmanuel ta ce:
"Mu nemota don Allah sannan mu tattara mata kudi. Kada Allah yasa Najeriya ya faru da wani daga cikinmu."
Babyshynie ta yi martani:
"Wayyo Allah ku taimaka mata, ku kai ta ofishin Sanwo Olu. Zai daura daga nan."
Chiamakaugoo ta yi martani:
Pa Tinubu na yi kamar mai daukar fansa kan 'yan Najeriya. Lokacinka ne ka samu baka shirya ba. Abun takaici."
Tsadar kaya: Bashir ya magantu kan rufe kantin Sahad
A wani lamari na daban, Bashir Ahmad, tsohon hadimin tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi martani kan rufe kantin Sahad, babban kanti a yankin Garki da ke Abuja.
Ahmad ya ce baya tunanin akwai kantuna da yawa masu saukin kaya kamar na Sahad a babban birnin tarayya.
Asali: Legit.ng