Kotun Musulunci Ta Aika Ramlat ‘Yar TikTok Zuwa Kurkuku a Kano, An Bayyana Dalili
- Bayan gurfanar da 'yar TiokTok, Ramlat Mohammed, alkali ya yi umurnin garkame ta a gidan gyara hali
- Alkalin kotun musulunci da ke unguwar Sharada, Mai Shari’a Sani Tanimu Hausawa ya yi umurnin tsare Ramlat kan koyar da karuwanci
- Hukumar Hisbah ce ta gurfanar da matashiyar bayan ta yi bidiyon cewa dole mijin da za ta aura ya barta ta auro tata matar
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Jihar Kano - Bayan sauraron korafin da aka shigar kan fitacciyar 'yar TikTok, Ramlat Mohammed wacce aka fi sani da Ramlat Princess, rahoto ya nuna alkali ya garkame ta.
Jaridar Aminiya ta ruwaito a ranar Juma'a, 16 ga watan Fabrairu, cewa alkalin kotun musulunci ya yi umurnin tsare Ramlat Princess.
Wasu laifuka ake tuhumar Ramlat a kai?
An garkame fitacciyar jarumar ne a gidan gyara halui kan zagin da ake yi mata na koyar da karuwanci da badala.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A daren Juma’a ne Mai Shari’a Sani Tanimu Hausawa na kotun Musuluncin wacce ke zama a unguwar Sharada ya sa a tsare Ramlat bayan Hukumar Hisbah ta gurfanar da ita a gabansa.
Wannan matakin ya biyo bayan ganin bidiyon matashiyar a soshiyal midiya, inda a ciki take tallata madugo, tare da alakanta kanta da muguwar dabi'ar.
A cikin bidiyon dai, Ramlat ta bayyana cewa duk mijin da za ta aura dole ya kyale barta ta auro tata matar, lamarin ya haddasa cece-kuce tsakanin al'umma, rahoton Leadership.
Matsayin laifin da Ramlat ta aikata
Takardar karar ta bayyana cewa an sami jarumar da yin amfani da kafar sada zumunta wajen yada kalaman badala.
A cewar takardar kara laifukan da ake tuhumarta a kai sun ci karo da sashi na 341 da 275 da 227 na Kundin Pinal Kod.
Wacce ake zargin ta amsa laifukan inda ta nemi afuwar kotu bisa laifukan da ta aikata.
Sai dai saboda kurewar lokaci kotun ta dage shari’ar zuwa ranar 19 ga Fabrairu don yanke hukunci.
Daga karshe kotun ta dage shari'ar zuwa ranar 19 ga watan Fabrairu don yanke hukunci, sannan ta yi izinin tisa keyar mai laifin zuwa gidan gyara hali.
Jaridar Legit ta ji ta bakin wata Bakunuwar mata mai suna Malama Binta Labaran kan ayyukan 'yan Hisbah a jihar Kano.
Malama Binta Labaran ta ce:
"Muna maraba da jin dadin wadannan matakai na 'yan Hisbah ko don tarbiyar 'ya'yanmu da kannenmu, ace 'yan mata sun zama babu kamun kai suna sakin zantuka yadda suka ga dama don neman suna.
"Barin irin su Ramlat, Murja da sauransu cikin al'umma babban hatsari ne, wannan kadai ya isa ya sa bala'i su dunga saukar mana saboda sakacin wawayen cikinmu."
Gwamnatin Kano ta janye lasisin Amart
A wani labarin, mun ji cewa hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta kwace lasisin wasu kamfanoni biyu mallakin Aisha Tijjani wacce aka fi sani da Hajiya Amart.
Ta hanyar soke lasisin ta, yanzu an dakatar da Amart daga baje kolin fina-finta ko rarrabawa, da kuma sa hannu a ayyukan masu tura fina-finai a cikin jihar.
Asali: Legit.ng