Tsadar Kaya: Tsohon Hadimin Buhari Ya Magantu Yayin da Gwamnatin Tinubu Ta Rufe Babban Kanti a Abuja

Tsadar Kaya: Tsohon Hadimin Buhari Ya Magantu Yayin da Gwamnatin Tinubu Ta Rufe Babban Kanti a Abuja

  • Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ba lallai 'yan Najeriya su fahimci dukkan dalilan da suka sanya aka rufe kantin Sahad ba
  • Hukumar kula da kare hakkin masu amfani da kayayyaki ta kasa (FCCPC) ta rufe babban kantin nan na siyar da kaya da ke yankin Garki Abuja
  • A cewar Ahmed, kantin Sahad na daya daga cikin masu saukin kaya a Abuja kansacewar farashin kayansu na iya tsayawa a inda yake tsawon watanni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Bashir Ahmad, tsohon hadimin tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi martani kan rufe kantin Sahad, babban kanti a yankin Garki da ke Abuja.

Ahmad ya ce baya tunanin akwai kantuna da yawa masu saukin kaya kamar na Sahad a babban birnin tarayya.

Kara karanta wannan

Tsadar abinci: Gwamnati ta rufe wani babban kanti a Abuja, an samu cikakken bayani

Bashir Ahmad ya ce kantin Sahad na da saukin kaya a Abuja
Tsadar Kaya: Tsohon Hadimin Buhari Ya Magantu Yayin da Gwamnatin Tinubu Ta Rufe Babban Kanti a Abuja Hoto: @BashirAhmaad/@Imranmuhdz
Asali: Twitter

Tsohon hadimin Buharin ya bayyana hakan ne a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) @BashirAhmaad a ranar Juma'a, 16 ga watan Fabrairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewar farashin kaya a Sahad yana iya tsayawa inda yake tsawon watanni, sabanin sauran kantuna da ke yawan sauya farashinsu.

Sai dai kuma, ya ce hukumar FCCPC ta fi yawancin 'yan Najeriya sanin dalili.

Ya ce:

"Yayin da ba lallai ne mutum ya fahimci duk dalilan da suka sa aka rufe kantin Sahad ba, amma dai suna cikin mafi inganci a Abujan nan. Ba na tunanin akwai kantuna da dama da farashi mai sauki da ya fi nasu.
"Farashin wajen na iya tsayawa tsawon watanni, sabanin wasu kanti da dama da ke yawan sauya farashinsu kusan kullun.
"Ya kamata a lura cewa hukumar kula da farashin kaya na gwamnati ta san dalili fiye da yawanci mutane."

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta kafa hukumar kayayyakin masarufi don daidaita farashin kayan abinci

'Yan Najeriya sun yi martani

@hansatua

"Da farko, ba mu san ainahin dalilin da yasa aka rufe shi ba kuma bai kamata mu yanke hukunci ba. Duk wanda ya taba zuwa wajen nan ya san sun fi saukin farashin kaya.

@layhamoh

"1 daga cikin dalilai da ba a sani ba....wani mutum ya siye dukkan buhuhunan sikari daga kantin makonni 3 da suka gabata wanda nan take ya haifar da tsadar farashin sikari na fitar hankali. ‍♀️
"Amma eh su ke da farashi mafi kyawu a fadin kantuna a Abuja."

@DanjumaPara

"Gaskiya fa har yanzu ban fahimta ba saboda suna tsayawa kan farashinsu tsawon shekaru."

Gwamnatin tarayya ta rufe kantin Sahad

A baya mun ji cewa kasa da awanni 24 bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya ba jami'an tsaro umarnin kamasu masu boye kayan abinci, hukumar FCCPC ta fara aiki.

Hukumar wacce ke kula da kare hakkin masu amfani da kayayyaki ta tarayya, ta rufe babban kantin Sahad da ke Garki, a babban birnin tarayyar, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng